Ba Hukuma Kadai Tsaro Ya Rataya A Wuyanta Ba – Hon. Wadata     

- Advertisement -

Ba Hukuma Kadai Tsaro Ya Rataya A Wuyanta Ba – Hon. Wadata      

Daga Jamil Gulma,

Honarabul Wadata Muhammad Maikulki  (Dan Isan Binji) shugaban karamar hukumar mulki ta Binji ya yi kira ga al’umma da su sa ido tare da Kai rahoton duk wata bakuwar fuska da suka gani a cikin yankunan su.

Ya yi wannan bayanin ne jiya a garin Binji jim kadan bayan kammala Sallar Idi inda ya bayyana cewa shi fa labarin tsaro ba na gwamnati kadai ba ne ya rataya a kan kowane mutum saboda haka ya kamata kowa ya saka ido tare da kai rahoton duk wata bakuwar fuska ko kuma wani gungun mutane da ba a yarda da su ba.

Ya kuma yi amfani da wannan damar ya yi kira ga iyaye da su kai yaransu makaranta domin samun ilmin addini da na zamani musamman saboda wannan gwamnati mai ci yanzu ta baiwa bangaren ilmi fifiko inda  ta yi tanadin kayan aiki da fadada makarantu kuma ba da dadewa ba ta  dauki kwararrun malamai dubu biyu don karawa bisa ga wadanda a ke da su.

- Advertisement -