Ba Da Tallafi Ba Sai Mai Kudi Ba, Ko Maraya Daya Ka Sami Dama Ka Tallafa Masa – Shattiman Dambo

- Advertisement -

Ba Da Tallafi Ba Sai Mai Kudi Ba, Ko Maraya Daya Ka Sami Dama Ka Tallafa Masa – Shattiman Dambo

Wakilinmu ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami damar tattaunawa da wani matashin dan siyasa a jam’iyyar APC ALHAJI MUSA DALLADI, wanda kuma shi ne Shattiman Dambo a karamar Hukumar Zariya. Ya tattauna da shi ne jim kadan bayan kammala rarob kayan tallafi abinci da tufafi ga marayu da sauran al’umma marasa karfi domin samun damar ci gaba da azumi da kuma bukukuwan Sallah cikin natsuwa, kamar yadda sauran yara da su ke wasu sassa da dama a karamar Hukumar Zariya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so jin dalilian da suka sa ka rarraba wannan tallafin kayayyakin abinci?

A gaskiya wannan tallafi da ku ke magana a kai, mun dade mu na yinsa, domin na shafe shekara fiye da 25 na yinsa a duk lokacin da suka dace, ba lallai lokacin azumi ba, tun ina yi dan kadan, har Allah cikin ikonsa ya ba ni damar fadada wannan tallafi ga al’umma da suka hada da marayu da sauran al’umma da mu ka lura su na bukatar tallafin abin da za su ci da tufafin da za su sanya.
Kuma baya ga kayayyakin abinci da tufafi da aka rarraba a yau, shekaru da dama solar tsara wasu hanyoyi da mu ke aiwatar da koyar da yara maza da mata karatun yadda za su rubuta jarabawa ta ko wane mataki na ilimi, inda na ke daukar nauyin koyar da yaran da kuma kayayyakin koyar da su daruusan da su ke bukata, mun ga amfanin wannan aiki da mu ka yi a wannan gari na Dambo da sauran garuruwa da suke makotaka da wannan gari, domin yara da dama solar sami damar shiga makarantun gaba da firamare da kuma makarantun gaba da sakandare da suke ciki da wajen Jihar Kaduna.
Sauran ayyukan da na ke aiwatarwa domin ciyar da al’umma gaba da kuma warware ma su matsalolinsu, solar hada da yin gadoji a wuraren da ake bukata da gyaran hanyoyi musamman a lokutan damuna da lalacewar hanyoyi na kawo matsaloli ma su yawa ga al’ummomi da suke bin hanyoyin.

To ya ka ke jin bayanan al’umma kan ayyukan tallafin da ka ke yi?
A gaskiya godiya da kuma sa albarka da al’umma ke yi gareni da sauran wadanda suke tallafa mani wajen ayyukan da na tsara su ne kan gaba da a duk rana na ke aiwatarwa domin ciyar da al’umma gaba, kamar yadda na bayyana a baya, suna sa albarka na kara ma ni kwarin gwiwar ci gaba da tallafa wa al’umma fiye da tunanin mai tunani.

A nan, wasu shawarwari za ka mika ga al’umma kan halin tsadar rayuwa da ake ciki a yau ?
Babu ko shakka, shawara da kuma kiran da zan yi ga al’umma shi ne, batun bayar da tallafi, ba sai mai kudi kawai ba, ko da mutum daya ko maraya daya mutum ya sami damar tallafa masa, Allah ya san ya yi abin da zai iya ne, haka ma in ya tallafa wa mutum daya da ke neman tallafi, a wajen Allah ya yi abin da zai iya ne. Amma batun sai ma su dukiya kawai za a sa ma su yi wajen tallafa wa al’umma, musammam marayu, wannan babban kuskure ne day a dace al’umma su dauki matakin gyara, domin al’umma da su ke cikin matsaloli da marayu su sami mafita a tsadar rayuwar da suke ciki.
Saboda haka, ina jawo hankalin marasa karfin da ma su karfin, kowa ya yi abin da zai iya, domin ya yi tallafin shi ma Allah zai ci gaba da tallafa ma sa, fiye da abin da ya fitar daga cikin abin da ya mallaka na dukiya ko kuma na tufafin da al’umma suka mallaka.

Wani irin tallafi ya dace al’umma su fi mayar da hankali a kai musamman ga marayu maza da mata?

Baya ga ba su abinci da tufafi, a kuma duba yadda za a gina rayuwarsu, na samar ma su da yadda za su koyi sana’o’in dogaro da kai, wanda in solar iya sana’a, wata rana za su dogara da kansu, in solar fara sana’o’in kuma su rike kansu su kuma tallafa wa sauran al’umma su ma ta hanyar koya wa yara da suke da iyaye sana’o’in da suka iya.
Kuma ya na da kyau, a rika kula da tallafa wa maraya ya sami ingantaccen ilimi bayan an tallafa ma sa ya sami ilimin sana’a, wannan ma, zai matukar tasiri ga marayun su kasance solar tsira daga taragon wadanda ke jiran a ba su tallafin abinci ko kuma tufafi da a yau su ne al’umma suka fi mayar da hankali a kai, to lokaci ya yi da za a yi gyara da zai zama an sami yadda za a rika rage yawan marayun da suke jirar a ba su tallafi.

Wane tunani ka ke da shi ga iyayen da suke rike da marayu?
A gskiya na fara tunanin fitar da tsarin ganin samar da sana’o’in dogaro kai ga kiyaye mata da suke tare da marayu, domin a kwai kananan sana’o’I da in an tallafa wa iyayen marayu, babu ko shakka, dan lokaci kadan iyayen marayun za su tashi daga ma su jirar a tallafa wa marayunsu, sana’o’in da suka iya, za su rungumi marayunsu da hannu biyu da kuma warware ma su duk wata matsala da ta ke addabarsu, ba tare da solar jira wani tallafi ba.

A kwai kishin kishin da mu ka ji cewar al’umma na zawarcin ka ka yi takara a zabe mai zuwa, shin haka ne ?
Babu shakka a kwai wannan labari, kamar yadda na bayyana ma ku tun a baya, fiye da shekara 25 mu ke aikin tallafa wa al’umma a fannoni da dama, lallai al’umma solar bukaci mu nemi damar wakiltarsu a karamar Hukumar Zariya, tun dama duk abin da mu ke yi al’umma mu ke yi wa, tun da mun fara samun mafita, sai mu ka ga ni’mar da Allah ya yi ma na bai dace ni’imar tsaya gare mu ba, sai mu ka fara mika ni’imar ga al’umma na kusa da nesa da marayu da kuma mabukata, mu na tunanin yadda al’umma suka ga mun damu da su, shi ya sa suka nemi mu yi ma su wakilcin, mu na shirye mu yi abin da al’umma ke bukata in da zai zama alheri garesu da kuma garemu.

- Advertisement -