Ba Da Jimawa Ba Zan Bayyana Makomata -Zidane

- Advertisement -

Ba Da Jimawa Ba Zan Bayyana Makomata -Zidane

Kocin kungiyar kwallon kafa taa Actual Madrid, Zinedine Zidane, ya musanta rahotannin da ke cewar zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana sai dai ya ce nan gaba kadan zai bayyana inda zai koma .

 

Zidane  ya fadi haka ne, bayan kammala wasan da Actual Madrid ta je ta doke kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao da ci 1-Zero a wasan mako na 37 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

 

Actual Madrid wadda ke takarar kare kofin La Liga, tana mataki na biyu da maki 81 da tazarar maki biyu tsakaninta da Atletico mai jan ragama kuma sai a ranar Lahadi 23 ga watan nan na  Mayu za a karkare wasannin mako na 38 kuma na karshe a gasar La Liga ta bana, shi ne za’a tantance wadda za ta lashe kofin kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021.

 

Zidane ya ce ya mayar da hankalinsa kan wasan da Actual Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Billareal ranar Lahadi a gasar ta La Liga kuma tun farko wasu jaridu ne a Spaniya suka wallafa cewar kocin ya shaida wa ‘yan wasa cewar a kakar bana zai bar kungiyar, batun da ya ce ba gaskiya ba ne.

 

Zidane ya ja ragamar Actual Madrid karo na biyu kenan, bayan da ya lashe kofin zakarun turai na Champions League har guda uku a jere daga lokacin da ya fara aiki tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2018.

Zidane ya sake komawa horar da Actual Madrid karo na biyu, bayan da kungiyar ta sallami mai koyarwa Julien Lopetegui da kuma Santiago Solari, daga nan ya lashe La Liga a bara kakar shekara ta 2019 zuwa 2020.

Sai dai kuma wasu na hasashen cewar watakila idan bai dauki kofi ba a kakar nan zai fuskanci kalubale daga wajen mahukuntan kungiyar saboda a wannan kakar Actual Madrid ta rasa gasar Copa del Rey da Spanish Tremendous Cup da kuma Champions League wanda Chelsea ta fitar da ita a kakar nan.

A zantawarsa da manema labarai  bayan tashi daga wasan da kungiyar tasa ta samu nasara, Zidane yace bai gayawa ‘yan wasa cewa zai bar kungiyar ba kuma sai an kammala kakar wasa zai bayyana makomarsa.

 

- Advertisement -