Ba Da Jimawa Ba Nijeriya Za Ta Zama Cibiyar Zaman Lafiya A Afirka – Osinbajo

0
131

Ba Da Jimawa Ba Nijeriya Za Ta Zama Cibiyar Zaman Lafiya A Afirka – Osinbajo

Daga Yusuf Shu’aibu

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa yana da tabbacin Nijeriya za ta zama cibiyar zaman lafiya da cikakken tsaro da ci gaba wanda ba a taba samu ba a Nahiyar Afirika.
Mataimakin shugaban kasan ya furta hakan ne a ranar Lahadi a garin Abuja, wajen baban taron shekara-shekara karo na 108, na cocin Baptist wanda ya gudana a Jihar Legas.
Mista Osinbajo ya ci gaba da bayyana cewa, Nijeriya za ta kasance mai samun bunkasar tattali arziki da samun nasarar kakkabe matsalolin da suka addabi kasar, saboda akwai alkawarin Allah a kan kasar na za ta zama wurin zaman lafiya da tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba samu ba a Nahiyar Afirika.
Ya kuma bayyana cewa, ba mai iya ja da lamarin Allah ko wane ne shi. Ya kara da cewa,“Ina da cikakken yakinin cewa babu wani ko wata kungiya ko wata akida da za ta iya karya alkawarin Allah don ci gaban Nijeriya.”
Mai magana da yawun Osinbajo, Mista Laolu Akande ya bayyana cewa, Farfesa Osinbajo ya kara da cewa, “Nijeriya za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu a kai.
A cewarsa, ana iya ganin hakan kamar ba zai yuwu ba, amma a wajen Allah babu abin da ba zai yuwu ba. Mataimakin shugaban kasa ya bukaci mahalarta taron maza da mata da su amince da wannan lamari domin su fita cikin shakka.
Kalaman na mataimakin shugaban kasa na zuwa ne yayin da kasar ke ci gaba da fama da kalubale na rashin tsaro da dama. kasar na fuskantar matsaloli kamar tayar da kayar baya a Arewa-Maso-Gabas, ‘yan ta’adda a yankin Arewa-Maso-Yamma da tayar da zaune tsaye a Kudu-Maso-Gabas da rikicin Fulani -makiyaya a dukkan yankin na tsakiyar Arewaci da kuma jihohin Kudu-Maso-Yamma da dama.

What's On Your Mind?