Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba, Inji Sarkin Musulmi

- Advertisement -

Ba A Ga Watan Karamar Sallah Ba, Inji Sarkin Musulmi

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,

Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’advert Abubakar III ta bayyana cewar ba a samu ganin jinjirin watan Shauwal 1442AH ba don haka watan Ramadan zai yi kwana 30, a yi Sallah ranar Alhamis.

Kwamitin Bayar da Shawara Kan Harkokin Addinin Musulunci wanda Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ke jagoranta tare da hadin guiwar Kwamitin Ganin Wata na Kasa ne ya bayyana hakan a takardar manema labarai a daren nan.

“Yau Talata 11 ga Mayu wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1442AH mai albarka ba a samu ganin jinjirin watan Shauwal a ko’ina a fadin kasa ba, don haka gobe Laraba 12 ga Mayu ita ce 30 ga Ramadan.”

“Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya aminta da rahoton ya kuma bayyana ranar Alhamis 13 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Shauwal, ranar Sallah Karama.” In ji bayanin.

A kan wannan, Sarkin Musulmi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci-gaba da yi wa kasa addu’a domin samun zaman lafiya tare da kira ga al’umma da su ci-gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da suka gudanar a watan mai tsalki.

Tun da farko dai Mai Alfarma Sarkin Musulmi a ranar 10 ga wata ta hannun Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid wanda shine shugaban kwamitin bayar da shawara Kan Harkokin Addini ga Majalisar Sarkin Musulmi ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin kasar nan da su fara duban watan Shauwal a ranar Talata 11 ga wata tare da bayar da rahoton ganin wata ga iyayen kasa mafi kusa ko Fadar Sarkin Musulmi.

Tuni dai Kasashe da dama a fadin duniya suka bayyana sanarwar yin azumi 30 a dalilin rashin ganin wata. Kasashen sune Saudi Arabia, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkey, Qatar, Malaysia, Indonesia da Jordan.

- Advertisement -