Ayyukan Ci Gaba Da NIS Ke Yi Sun Amsa Sunansu A Duniya – Sabon Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida

0
67

Sabon Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida, Dakta Shuaibu Belgore ya jinjina wa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede bisa ayyukan bunkasa kayan additional rayuwa da sauye-sauye na zamani da hukumar ke aiwatarwa.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar aiki a shalkwatar hukumar ta NIS da ke Abuja.

Dakta Belgore ya yi bayanin cewa duk abubuwan da ya gani na zamani ne masu kyau irin na kasashen da suka ci gaba a duniya. Ya hori hukumar ta kara zage damtsen aiki a matsayinta ta hukumar da ke taka rawa a bangaren tsaro, kana ya tabbatar wa da CGI Babandede samun goyon bayansa.

Ayyukan Ci Gaba Da NIS Ke Yi Sun Amsa Sunansu A Duniya

Da yake zagayawa da Babban Sakataren wasu daga cikin sababbin ayyukan ci gaba da NIS ta aiwatar aka kaddamar da su da kuma wadanda ake kan gudanarwa a shalkwatar hukumar, CGI Muhammad Babandede ya yi masa bayani sport da hukumar ta NIS da irin aikace-aikacenta. Wakazalika, ya bayyana kudirin hukumar na ci gaba da aiwatar da abubuwan da za su yi tasiri a ma’aikatar da kuma kasa bakidaya.

Sheikh Bala Lau yayi kira ga masu ce-ce kuce akan Gayyatar Sheikh Jingir zuwa Hadejia, da su daina

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James ya fitar ta ce daga cikin sassan aiki da Babban Sakataren ya ziyarta akwai sabon zauren taro na hukumar, da cibiyar aikin fasfo ta zamani, da cibiyar rajistar baki ta zamani, sashen kula da horas da jami’ai, sansanin manyan jami’ai, katafariyar ma’ajiya da kuma sabon katafaren ginin fasahar sadarwa ta zamani.

Har ila yau, sauran photo voltaic hada da gidan mai, masaukin kananan ma’aikata, sashen kanikanci, cibiyar aiki da rundunar ‘yan sandan duniya da ke aiki dare da rana da cibiyar sanya ido da bayar da umurni da sauransu.

What's On Your Mind?