Ayarin Shehu Kusfa Zariya Ya Ziyarci Sharif Abba Garun Ali Kano

- Advertisement -

Ayarin Shehu Kusfa Zariya Ya Ziyarci Sharif Abba Garun Ali Kano

Daga Mustapha Ibrahim,

Babban Shehun Daridar Tijjaniya Sheikh Usman Kusfa Zaria ya jagoranci ayarin sharifai da shehunai da malaman Tijjaniya daga Jihohin daban-daban na Arewa kamar Bauchi, Maiduguri, Yobe, Gombe, Sokoto, Zamfara da sauransu da suka ziyarci Sharu Haruna Abba Garun Ali domin sadar da zumunci na ziyartar waliyai bayin Allah wadanda suke raye da kuma wadanda suka yi wafati, kamar dai yadda wannan ayari na Shehun Kusfa na Zaria kamar yadda suka saba yi.

Sharu Haruna Abba Garun Ali ya bayyana cewa wannan ziyara ta Shehunai da Waliyai an dade ana yin ta duk shekara ta yadda ake ziyartar shehunai da malaman Tijjaniyya irin su Sani Kafunga, irin su Shehun Salga da Shehun ‘Yan Mota, da Shehu Mai Hula da kuma shehunai daban-daban dake kasar nan irin su shehunan darika na Bauchi tun shekaru aru-aru da sauran waliyai da shehunan tijjaniya na kasar nan, wanda ya ce wasu ana ziyartar su ne a makwancin su da kuma yi musu addu’ar jaddada neman rahama gare su dan haka ziyarar ta hada gidajen shehunai da waliyay a gidajen su da kuma makwantan su wadanda sukayi wafati a cewar Sharu Haruna Abba Garun Ali.

Har ila yau ya koka da yadda sharifai ahlul baiti ke fuskantar kalubale wanda ya samo asali tun daga kan wafatin Manzon Allah (S.A.W) na abun da ya faru ga sharifai ahlul baiti ya faru daga wasu wanda basu fahimci ahlul baiti ba kuma tun wannan lokaci ahlul baiti sharifai ke fuskantar kalubale ta hanyar kin taimakawa sharifai daga  gwamnatoci  da sauran mawadata da sauran al’umma a cewar Sharu Haruna Abba Garun Ali.

Har ila yau ya kara da cewa ba wani abu ne ya sa sharifai ahlul baiti a yanzu suke fuskantar matsaloli ba ssai rashin gane su waye sharifai na hakika da kuma hadin kai ga su sharifan na hakika domin daukaka da daraja da dake tare da sharifai a yau ya sa makaryata solar yi yawa da sunan sharifai ahlul baiti domin matsayi ne mai daraja da daukaka wanda hakan ce tasa ake karya da sharufta don a samu daular duniya da daukakar duniya wanda ya sa ake karya da sharufta wanda kuma sune suke kawo cikas wajen hada kan sharifai a wannan zamani.

 

A karshe Sharu Abba ya ce ko da yake mu ba alfahari ba godiyar Allah ce ta sa mu bamu daga cikin wadanda muke bukatar a taimaka mana domin Allah ya azurta mu da abin da ya bamu amma muna san a taimaka ma sharifai ahlul baiti ta kowanne fanni domin samun yardar Allah kuma muna kira ga gwamnatoci da ‘yan kasuwa akan kokarin kawo sassauci da sauki ga al’umma ta fuskar saukaka farashi kayan masarufi da taimakon al’umma marayu da raunana musamman a wannan lokaci da komai ya tsawwala.

- Advertisement -