AU Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da TikTok Domin Gudanar Da Bikin Ranar Afirka

- Advertisement -

AU Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da TikTok Domin Gudanar Da Bikin Ranar Afirka

Daga CRI Hausa

Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta ce za ta yi hadin gwiwa da kamfanin fasaha mai manhajar raba kananan bidiyo na TikTok, domin gudanar da shagulgulan ranar Afirka ta amfani da yanar gizo.

A cewar shugaban hukumar Moussa Faki Mahamat, za a gudanar da bikin na tsawon rabin wata ne bisa taken “Ni dan Afirka ne,” wanda kuma zai hallara sassan matasa mata, da masu rajin daidaiton jinsi. Ana kuma sa ran hadin gwiwar zai ingiza manufar AU mai lakabin “Matasa miliyan daya nan da shekarar 2021”, wadda ke kunshe da burin AU, na samarwa matasan Afirka damar cin gajiya a fannonin ilimi, da guraben ayyukan yi da sana’o’i.

Kaza lika shirin zai zaburar da gangamin nahiyar Afirka mai lakabin “Ni dan Afirka ne,” wanda a bana ke da taken “Al’adu da abubuwan da aka gada, Gina irin Afirka da ake fata.” (Saminu)

- Advertisement -