Atisayen ‘Murmushin Kada IV’ Ba Shi Da Alaka Da Zanga-zangar #ENDSARS – Rundunar Soji

0
49

Atisayen ‘Murmushin Kada IV’ Ba Shi Da Alaka Da Zanga-zangar #ENDSARS – Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce sabon aikin atisayen murmushin kada na hudu ‘Crocodile Smile Iv’ ba shi da wata alaka da zanga-zangar #ENDSARS da ke gudana yanzu haka a fadin kasar nan.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kanal Sagir Musa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi jiya a Abuja.

Musa ya jaddada cewa atisayen biki ne na shekara-shekara da aka shirya don horar da manyan jami’an soji da kananansu a kokarin rundunar na tabbatar da tsaron Najeriya da ‘yan kasa.

Na Ɗauki Kirista Fiye Da Musulmai A Matsayin Ma’aikata – Isa Pantami

“Wannan atisaye ne na shekara-shekara a cikin littafin tsare-tsaren rundunar wanda a al’adance ake farawa daga Oktoba zuwa Disamba na kowace shekara.

A cewar Musa, atisayen na bana an tsara shi ne daga 20 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba, kuma ba shi da wata dangantaka da duk wata zanga-zangar lumana ta kowane irin yanayi.

Ya mayar da martani ne ga masu ce wa rundunar ta fara atisayen ne da nufin dakile zanga-zangar #ENDSARS, wannan zargi ba dai-dai ba ne.

“Rundunar sojin ta umarci duk ‘yan Najeriya masu bin doka da oda da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata tsangwama ba,” in ji shi.

What's On Your Mind?