2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

0
71

Tsohon mataimakin Shugaban-ƙasa, Atiku Abukar, ya magantu a kan bayyanar wasu fastocin yaƙin neman zaɓensa da suka mamaye yanar-gizo tun satin da ya gabata.

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Litinin, Atiku, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, ya nesanta kansa daga bullar fastocin.

A jikin fastocin, an gabatar da Atiku a matsayin mutum na kwarai da zai iya ceton Najeriya.

Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, a yayin da yake maida martani a kan batun, ya ce hankalinsa yafi karkata wajen ganin jam’iyyarsa ta PDP ta samu nasarar lashe zaɓen jihar Ondo.

Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

Martanin ya fito ne ta hannun mai yaɗa labaran Atiku, Paul Ibe.

Acewar Ibe:”lokaci na ƙarshe da nayi magana, na ce Atiku a halin-yanzu yafi karkarta ga zaɓen Edo.

”Kuma mun gode Allah mun gama da Edo, PDP ta yi nasara.

“Yanzu, Atiku da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, solar duƙufa a kan zaɓen jihar ondo.

”Dukkanin waɗannan zaɓuka suna da muhimmanci saboda suna ƙarawa jam’iyyarmu ƙarfi a zaɓe mai ƙaratowa a shekarar 2023.

“Wannan ba shine lokacin tsayawar Atiku ba, ba batun zaben shekarar 2023 ake yi a halin yanzu ba”

“Kodayake, ko dama Atiku zai ƙara tsayawa neman takarar shugabancin ƙasa, ba zai fitar da fastoci ba tun yanzu”

”Kada mu yi riga malam masallaci da azarɓaɓi, mu fara gamawa da batun zaɓen jihar Ondo da ke gab da ƙaratowa”A cewar Ibe.

What's On Your Mind?