Ana ci gaba da martani a kan rasuwar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso
Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jinjina kyawawan dabi’un marigayin
Marigayi Saleh Kwankwaso ya kasance jigo da ake ganin mutuncinsa a jihar Kano
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya mika ta’aziyya ga iyalan Kwankwaso a kan mutuwar Musa Saleh Kwankwaso.
Marigayin ya kasance uba ga tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.
Atiku ya ce marigayin ya kasance mai sadaukarwa addininsa, iyalai da jama’a.
Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya yi addu’an Allah ya ji kan marigayin.
Da farko mun ji cewa majidadin masarautar Karaye kuma hakimin karamar hukumar Madobi, Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya, kamar yadda Every day Nigerian ta rawaito.
Marigayin shine mahaifi wurin tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya.
Every day Nigerian ta rawaito cewa sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya tabbatar mata da rasuwar basaraken sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.
My thoughts and prayers are with the Kwankwaso family on the loss of their patriarch. The late Alhaji Musa Saleh Kwankwaso lived a long and impactful life. He was devoted to his religion, family and society. I condole with my brother, Sen. Rabiu Kwankwaso. pic.twitter.com/Cb9ikIBdUx
— Atiku Abubakar (@atiku) December 25, 2020
143 total views, 1 views today
Be the first to comment