ASUP Ga Gwamnatin: Ba Za Mu Janye Yajin Aiki Sai An Ba Mu Naira Biliyan 19

- Advertisement -

ASUP Ga Gwamnatin: Ba Za Mu Janye Yajin Aiki Sai An Ba Mu Naira Biliyan 19

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha (ASUP) ta bayyana cewa, ba za ta koma bakin aiki ba har sai gwamnatin tarayya ta cika mata bukatunta. A cewar kungiyar, bukatunta dai solar hada da, dole ne gwamnatin tarayya ta fitar da zunzurutun kudi na naira biliyan 15 na farfado da kwalejojin kimiyya da fasaha da ke fadin kasar nan da kuma karin wasu naira biliyan hudu domin biyan sabon tsarin karancin albashi ga mambobin kungiyar.

Shugaban kungiyar ASUP na kasa, Dakta Anderson Ezeibe shi ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labara a wannan mako. Ya bayyana cewa, ASUP a matsayinta na kungiya tare da mambobinta ba za ta bari gwamnatin tarayya tana yaudararta ba na yin alkawari a takarda domin ta janye yajin aikin da ta shiga. Ya kara da cewa, idan gwamnatin tarayya tana da gaskiya da cika alkawarin da ta yi wa kungiyar ASUP ta da biya wadannan kudade tun a ranar Talata da ta gabatar kamar yadda ta alkawarta. Ya ce, shugabannin kungiyar ASUP da wakilan gwamnatin tarayya solar tattauna a ranar Talata da ta gabata, inda gwamnati ta yi alkawarin za ta biya wadannan kudade cikin gaggawa. Ya ce, wakilan gwamnatin tarayya solar tabbatar da cewa, kafin wani karamin lokaci za a bai wa kungiyar kudaden ba tare da samun tsaiko ba.

“Amma tun daga ranar Talatar har zuwa ranar Jumma’a, gwamnati ba ta biya wadannan kudade ba da ta yi alkawari.

“Domin haka, muna ganin gwamnatin tarayya ta yi wannan alkawari a baki ne ba tare da niyyar biyan wannan kudi na biliyan 15 da za a farfado da kwalejin kimiyya da fasaha da ke fadin kasar nan ba da kuma kudaden da za a biya malaman na sabon tsarin karancin albashi.

“Za mu ci gaba da zama a gida har sai an cika wannan alkawari kafin mu dawo bakin aiki,” in ji shi.

Mista Ezeibe ya roki dalibai da iyaye da daukacin mutane da su fahimci kungiyar ASUP na gudanar da wannan yajin aiki. Ya ce, an yi hakan ne domin farfado da ci gaba harkokin ilimin kwalejin kimiyya da fasaha da kuma tattalin arzikin kasar nan.

A ranar Alhamis ne wannan yajin aiki na kungiyar ASUP zai cika wata daya daidai idan ba a sasanta ba kafin wannan rana.

- Advertisement -