Asibitin Magungunan Gargajiya Na Sin Dake Namibia Ya Samar Da Jinya Ga Mazauna Wurin

0
64

Asibitin Magungunan Gargajiya Na Sin Dake Namibia Ya Samar Da Jinya Ga Mazauna Wurin

Daga CRI Hausa

Wani asibiti dake ba da magungunan gargajiya na kasar Sin dake Windhoek, babban birnin kasar Namibia, ya kawo fata tare da inganta lafiyar mazauna wurin da dama.

Asibitin wanda ya fara aiki a 2018, ya samarwa marasa lafiya mugunguna kamar tsarin caccaka allurai, da kaho da tausa don karfafa gudun jini.

Likitan dake kula da asibitin Dr. Wang Peng, ya bayyana cewa, galibin cututtutan da asibitin ya ke kula da su, solar hada da gurmudewar baki, da rashin barci, da shanyewar wani bangare na jiki, da ciwon gwiwa da sauransu.

Wang ya ce, yayin kula da marasa lafiyan, yana mayar da hankali ne wajen ba su fata da kulawa mai kyau. Asibitin ya kuma taimaka wajen inganta lafiyar mazauna wurin, kamar yadda suka bayyana irin tasirin da asibitin na TCM ya yi a rayuwarsu.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?