Ashraf Mahmoud Massoud: Xinjiang Tana Samun Ci Gaba Da Kwanciyar Hankali

0
105

Ashraf Mahmoud Massoud: Xinjiang Tana Samun Ci Gaba Da Kwanciyar Hankali

Daga CRI Hausa

Ashraf Mahmoud Massoud, tsohon shugaban sashin Faransanci na gidan talabijin na kasa da kasa na kogin Nilu dake kasar Masar, ya wallafa wani sharhi recreation da jihar Xinjiang ta kasar Sin a baya-bayan nan, inda ya bayyana raayinsa cewa, gani ya kori ji dangane da batutuwan da suka shafi jihar. Ya kara da cewa, ya dace a saurari raayoyin wadanda suka taba ziyartar wurin, maimakon raayoyin wadanda ba su taba zuwa ba.

A kwanan nan ne, wasu kafofin yada labarai gami da yan siyasar kasashen yammacin duniya suka soki lamarin gwamnatin kasar Sin dangane da manufofinta kan jihar Xinjiang. A ranar 21 ga watan Afrilu, majalisar dokokin yankin dake amfani da harshen Faransanci a kasar Belgium ta zartas da wani kuduri, inda aka zargi Xinjiang da tilastawa maaikata aiki, da kafa sansanin bada horo. Kashegari kuma, wato 22 ga wata, majalisar wakilan Birtaniya ta zartas da kuduri, inda ake zargin cewa, wai yan kabilar Uygur gami da sauran yan kananan kabilu a Xinjiang suna fuskantar matsalar kisan kare dangi.
A hakika dai, akasarin yan siyasa gami da marubutan sharhi na kasashen yammacin duniya, wadanda suka zargi jihar Xinjiang, ba su taba ziyartar wurin ba, amma solar rubuta bayanai kamar solar taba ganin abubuwan dake faruwa a wurin ido da ido. Shin wannan hakikanin gaskiya ce ko kuma karya zalla? Ya dace yan jarida su fita daga ofisoshinsu, su nemi alummar Xinjiang don jin ta bakinsu, ko kuma neman mutanen da suka taba ziyartar Xinjiang, don kara fahimtar abubuwan da suka gani a wurin.
Idan an fahimci raayoyin wadanda suka taba ziyarar gani da ido a Xinjiang, zaa rubuta bayanan da suka shafi wurin, wadanda suka bambanta kwata-kwata da na kafofin watsa labaran yamma.
Tsohon mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar, Ali Al-Hefni ya taba zama jakadan Masar a kasar Sin daga shekara ta 2001 zuwa 2005. Ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, ya ziyarci Xinjiang, kuma kowace ziyararsa ta kai akalla yini uku. Ali Al-Hefni ya kuma nuna kwazo wajen samowa kamfanoni gami da cibiyoyin kasar Masar damammakin bunkasa harkokinsu a Xinjiang. A ganinsa, Xinjiang, wuri ne da kasar Sin take bude kofarta ga kasashen yammacin duniya. Bayan da kasar ta bullo da shawarar ziri daya da hanya daya, zuwa yanzu, Xinjiang na kara taka muhimmiyar rawa ta fuskar tattalin arziki kan sabuwar hanyar siliki.
Ali Al-Hefni ya yi karin haske cewa, a yayin ziyararsa a jihar Xinjiang, ko a babban birni Urumqi, ko kuma sauran wasu biranen dake bakin iyaka, ya ga manyan sauye-sauye. Abun da ya fi burge shi kuma shi ne, saurin ci gaban muhimman ababen extra rayuwar alumma a jihar, musamman hanyoyin mota da gine-gine. Ali Al-Hefni ya ce, dabarun kasar Sin na raya jihar Xinjiang abar koyi ce ga kasashe masu tasowa da dama, ciki har da ita Masar.
Sport da zargin da wasu kafofin watsa labarai da yan siyasar kasashen yamma suka yi dangane da batun Xinjiang, Ali Al-Hefni ya ce, ba abun mamaki ba ne, kuma za su ci gaba da irin wannan wayo a nan gaba. A cewarsa, in ba su yi amfani da batun Xinjiang ba, za su yi amfani da batutuwan da suka shafi Hong Kong da Tibet ko kuma Taiwan. Makasudinsu shi ne, haifar da rudani a kasar Sin, da jawo rashin fahimta tsakanin kasa da kasa, don kawo tsaiko ga dinkewar duk kasar baki daya.
Shi ma a nasa bangaren, mataimakin babban editan jaridar Ahram, wadda ita ce jarida mafi dogon tarihi da samun karbuwa a kasar Masar, Tarek Al-Senouti, ya taba ziyartar jihar Xinjiang sau uku. A nasa raayin, bayanan da kafofin watsa labaran kasashen yamma suka rubuta recreation da Xinjiang, solar sabawa gaskiya, kana akwai karairayi da kura-kurai masu yawa, musamman abun da suka ce wai ana cin zalin alummar Uygur, karya ce zalla.
Tarek ya ce, jihar Xinjiang ta kasar Sin tana girmama mabiyan kowane addini, akwai masallatai da coci-coci da wuraren ibada na addinin Buddah da dama a jihar. A cewarsa, ainihin makasudin kafafen yada labaran kasashen yamma shi ne, cimma muradunsu na siyasa. Ya kara da cewa, a ziyarce-ziyarcensa har sau uku a Xinjiang, shi da tawagogin kasashe sama da 30 solar ziyarci cibiyar aladun Islama, da babbar kasuwar Grand Bazaar, kuma ba su taba ganin wani abun da ya shafi cin zarafi ko lalata ba. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

What's On Your Mind?