Arewa Ta Zama Makabarta; Muna Cikin Wani Hali!

0
69

Arewa Ta Zama Makabarta; Muna Cikin Wani Hali!

Daga Yusuf Kabir, 09063281016:

Yanayin da muke ciki a halin yanzu, babu abunda yake damun mutanenmu na arewa fiye da batun rashin tsaro da ya addabi yankin  da wasu sassan wurare a kudancin Nijeriya.Tabarbarewar tsaro ta ta’azzara ainun ne a shekarar 2009 bayan an sami rikici tsakanin Almajiran Muhammad Yusuf da jami’an tsaro a Maiduguri.Tun daga wannan lokacin ne wannan yankin na arewa ya shiga halin ha’ula’in da muke gani a yanzu.

Dubban mutane ne suka yi hijira daga Barno zuwa wadansu Jihohi kamar Kano,Katsina Jigawa domin tsira da rayukansu.A tsakanin shekarar 2013-2014 garuruwan Maiduguri,Adamawa Yobe solar zamanto makabarta, a kullum sai an yi kisa ko an kona dukiya.A garin Potiskum din Jihar Yobe sai da ya zamanto banki guda kawai ya rage,sai da ya zamanto Masallaci guda daya kawai a ke sallar Juma’a a cikin sa.

Saboda fushin rashin samar da tsaro a garuruwan da muka ambata a sama,ya sa Talakawan Arewa suka zabi Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 da kyakykyawan  fatan za ta iya yiwa matsalar tsaro hadiyar kafinon.Tabbas an samu saukin tashe-tashen Bama-bamai a shekaru biyu na mulkin Buhari;amma bayan haka sai musibar garkuwa da mutane ta bullo gadan-gadan a yankin wacce ta addabi kowa!

Al’umma solar kauracewa bin manyan  hanyoyi da daman gaske saboda tsira da rayukansu.Hanyar birnin Gwari-Kaduna ta zamanto tarkon mutuwa ga duk wanda ya bi ta.Babbar jarabawa ga yankin arewa ma ita ce hanyar Kaduna-Abuja. Duk da ita ce babbar hanyar da za ta kai ‘yan Borno,Kano,Katsina,Jigawa,Yobe zuwa  babban birnin Tarayya Abuja,amma bin ta sai wanda ya sadaukar da rayuwarsa a yanzu.Sau nawa ana tare mutane a yi garkuwa da su a wannan hanya?Sau nawa masu garkuwa na kashe mutane a wannan hanya?Allah ne kadai ya san mutanen da aka kashe daga 2019-2021 a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin satin nan, mutanen Gaidam da ke jihar Yobe,solar kasance cikin firgici na tsawon lokaci,a yayin da mayakan Boko Haram suka mamaye garin.Gomomi solar yi hijira,a yayin da wadansu suka rasa rayukansu dungum a wannan garin,a yayin da dukiyar makuden kudade ta salwanta!

A na kukan targade sai karaya ta samu,domin kuwa Gwamnan jihar  Niger Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa Boko Haram solar kafa tutarsu a garin Shiroro wanda hakan babbar barazana ne ga Jihar da makwabtan ta.

Mutanen Jihar Zamfara kuma,a kullum sai an yi kisa ko an sace wani a Jiharsu.Ga muhimmin kira ga bagarorin nan dangane da matsalar tsaro:-

Gwamnati:

A kullum fafutikar ta kokarin samar da tsaro a kasar nan musamman ma yankin arewa;amma lallai akwai bukatar ta tashi tsaye haikan wajen kulawa da jami’an tsaro da tanadar musu kayan aikin da suka dace domin fuskantar matsalar nan.

2.Shugabanin Arewa:Nan ina magana da Gwamnoni,Sanatoci da ‘Yan majalissar wakilai,attajirai,Malamai ne,ya kamata ku motsa tun kafin a karasa ruguza wannan yankin naku.Ya kamata ku motsa tun kafin a yi wa Arewa sakiyar da babu ruwa.Ya kamata ku dauki mataki tun kafin abun ya kai ga matsalar ta shafe ku ku da iyalanku.

three.Sauran al’umma:A nan ina nufin talakawan wannan yanki ya kamata su shiga taitayinsu su yi wa kan su kiyamullaili tun kafin dare ya yi musu.Ya kamata mu zamanto masu tausayin kawunanmu,masu tallafawa junanmu,masu girmama ra’ayin junanmu,masu yi wa junanmu fatan alkairi.Ya kamata mu cire son kai,hassada,gaba a tsakaninmu kafin mu yi mutuwar tsaye.

Karkarewa

A cikin wannan watan na Ramadan mai albarka,ya zamanto wajibi a gare mu mu yawaita addu’o’i,sadakoki da istigfari ga ubangijinmu domin ya fitar da mu daga halin da muke ciki.

Sai mun hadu a wani jikon.

 

What's On Your Mind?