APPEALS Za Ta Tallafa Wa Manoma 50,000 A Jihar Kaduna

0
74

APPEALS Za Ta Tallafa Wa Manoma 50,000 A Jihar Kaduna

Shirin nan na APPEALS a jihar Kaduna ta bayyana cewa, za su hada kai da kungiyoyin manoma na jihar ta hanyar bayar da tallafi kai tsaye ga manoma 10,000 da kuma wasu manoma su 50,000 da suma za su amfana da tallafin don bunkasa harkar noma a jijar.

Shugaban shirin, Dr Yahaya Aminu, ya bayyana aka a yayin ziyararsa ga wasu kungiyoyin manoma a garin Zariya ranar Asabar.

Aminu ya kuma kara da cewa, suna kara karfafa al’umma na su kafa kungiyoyi a tsakanin su don suma su amfama da wannan tallafin da ake bayarwa.

Ya ce, samun kungiyoyin manoma a tsakanin al’umma zai taimaka wajen ganin an samar da tallafin da suka shafi hanyoyi da kuma kafa musu manyan injina da za su amfana da su wajen sarrafa kayan moman da suke shukawa.

“Mun lura cewa, manoman suna matukar sha’awar shirin kuma suna bukatar ganin photo voltaic samu karin yabanya da girbi a damuna mai zuwa a kan haka za mu taimaka musu.

“Mun kuma lura da matsalolin da suke fuskanta wadanda suka hada da rashin ingantaccen iri da kuma maganin kashe kwari da kuma rashin horaswa a kan hanyoyin mona na zamani.

“A kan haka za mu ci gaba da horas da su don su fara harkar noma a hanyoyin zamani, ta yadda za su samu karin kudaden shiga a tsakaninsu,’’ inji shi.

Ya kuma ce, a halin yanzu an fara shirin horas da manoman a kan hanyoyin ajiye bayanai na yadda aikinsu ke tafiya don su lura da abin da suke kashewa da kuma abin da yake shigo musu.

Tun da farko, ana ta jawabin, Kwamishinan Aikin gona da raya karkara, Hajiya Halima Lawal, ta ce, lallai shirin na da kayatarwa, ta kuma bukaci manoma su shigo don amfana da shirin, ta kuma yaba da abin da ta gani a karamar hukumar Zariya.

What's On Your Mind?