APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023 Saboda ‘Yan Nijeriya Na Son Ta –Tinubu  

0
184

APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023 Saboda ‘Yan Nijeriya Na Son Ta –Tinubu   

Daga Yusuf Shu’aibu,

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa, jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki har bayan shekarar 2023, soboda ‘Yan Nijeriya suna son jam’iyyar.

Tinubu ya yi wannan bayanin ne jim kadan bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke garin Abuja. Haka kuma ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, ko awa daya shugaban kasa Buhari ba zai kara ba idan wa’adin mulkinsa ya kare a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.

Ya ce ‘yan Nijeriya suna kaunar jam’iyyar APC kuma tana da damar ci gaba da rike madafun iko a matakin tarayya har bayan shekarar 2023. Ya ci gaba da cewa, ‘ya Nijeriya za su dawo kan layuka don zabar sabbin rukunin masu rike da mukaman gwamnati a dukkan bangarori a zangon farko na shekarar 2023.

 

Ya ce: “damar da muke da shi tana da haske kamar tauraruwar tsakar dare kuma za mu ci gaba da aiki don inganta Nijeriya.

 

“Ba za mu iya saka siyasa da hasashe a komai ba, muna da kasar da za mu gina.

 

“Ba za mu goyi bayar shugaban Buhari ban a kara koda awa daya a karagar mulki bayan shudewar wa’adin mulkinsa, domin hakan ya saba wa tsarin mulkin kasar nan,” in ji shi.

 

Jagoran jam’iyyar APC yi bukaci dukkan ‘yan kasa masu kyakkyawar manufa da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya a yayin da ake tsaka da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan kasar nan. A cewarsa, dole ne dukkan ‘yan Nijeriya su ajiye banbancinsu na addini da siyasa ko na kabilanci sannan su hada kai da jami’an tsaro don shawo kan matsalar tsaro a cikin kasar nan.

 

Ya ce, “kowacce kasa tana iya fuskantar irin matsalolin da Nijeriya take fuskanta a dai-dai wannan lokaci, amma muna ci gaba da tattaunawa da mutane da su yi hakuri da yanayin komi zai yi sauki, domin muna bin wasu dubarun canza salon shugabanci a cikin kasar nan.

 

“Ina kira da mu hada kai domin rage ayyukan ‘yan bindiga, domin da haka kai ne kadai za a iya samun inganta Nijeriya da kuma jin dadi da walwalar mutane.

 

“Muna kira da hada kai da fahimtar juna domin yana da matukar tasiri wajen samar da tsaro as cikin kasa.

 

A cewarsa, dukkan ‘yan Nijeriya suna cikin zuciyar shugaban kasa Buhari kuma baya son ganin su a cikin wannan matsalolin.

 

“Babu wani shugaban kasa da zai so ganin kasarsa da kuma mutanen kasar suna fama da hatsarin ‘yan bindiga. Haka kuma babu wani shugaba kasa da yake so kasarsa ta kasance cikin matsalolin bambancin kabilanci ko na addini da dai sauran matsalolin rashin tsaro.

 

“Kalubalan da ake fuskanta a halin yanzu yana bukatar tattaunawan gaggawa domin a shawo bakin zaran,” in ji shi.

 

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, cikin wadanda suka halarci ganawar sirrin da shugaban kasa Buhari a kan abubuwan da suke faru na rashin tsaro a yankin Arewa-Maso-Gabas. Zulum ya bayyana  ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a kwananin nan wajen yaki da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa –Maso- Gabas.

 

Ya ce, “bari in yi amfani da wannan dama in mika ta’aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

 

“Ina tunanin cewa nauyi ne da ya rataya a wutana in fada wa shugaban kasa gaskiya, domin ya san abubuwan da ke faruwa a gaba daya yankin Arewa-Maso-Gabas.

 

“Ina tunanin akwai bukatar mu samu gudummuwa domin mu sami nasara a kan yaki da ‘yan ta’adda.

 

“Abun takaici ne farmakin da aka kai wa garin Damasak da ke cikin Jihar Borno a ‘yan kwanakin nan, daruruwan mutane solar tsare daga gidajensu solar bar garin Damasak, haka ma abin da ya faru a garin Geidam da ke Jihar Yobe, mutane da yawa solar gudu daga matsuguninsu.

 

Jaridar The Nation ta ruwaito Tinubu yana fadin cewa, ya je fadar shugaban kasa tare da Cif Akande domin tuntubar shugaba Buhari kan hanyoyin magance matsaloli daban-daban da kasar nan ke fuskanta, inda ya bukaci dukkan ‘yan Nijeriya da su marawa gwamnati baya. A cewarsa, rashin jin dadin da ake ciki a yanzu ba za a iya cewa na musamman ba ne amma ya kamata a yi tarayya wajen samar da mafita, ta hanyar tuntuba da musayar ra’ayoyi kan yadda za a sauya arzikin kasar.

 

A wani labarin na daban kuma, Tinubu ya bayyana dalilai da ya say a rage zuwa fadar shugaban kasa, wanda ya ce babu abin da ya shiga tsakaninsa da Muhammadu Buhari.

 

An dai dauki tsawon lokaci Tinubu da Buhari ba su zauna kamar yadda suka saba ba, hakan ya sa ake rade-radin akwai rashin jituwa tsakanin shugaban kasar da Tinubu. A yanzu dai Tinubu ya bayyana cewa babu abin da ya shiga tsakaninsa da shugaban kasa Buhari.

 

“Babu wani sabani da ya shiga dangantakar da ke tsakaninmu. Wane ne ke duba alakarmu? Kafafen sada zumunta na zamani ne za su auna alakarmu?

 

Tinubu ya ci gaba da cewa, “ba na bukatar in addabe shi a gaban idanun kowa, haka ne? Yauwa, muna da hanyoyi da yawa da za mu iya fuskantar abubuwa.

 

“Akwai mutumci da kusanci da fada wa juna gaskiya ba tare da boye-boye ba a tsakanina da shugaban kasa,” in ji Tinubu.

What's On Your Mind?