APC Za Ta Shimfida Mulkin Shekara 32 – Buni

0
127

APC Za Ta Shimfida Mulkin Shekara 32 – Buni

Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC dake mulkin Nijeriya (CECPC) kuma Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, a jiya yake shaida cewar, jam’iyyar ta yi wani sabon tsarin da zai ba ta damar cigaba da mulkar Nijeriya har nan da wasu shekaru sama da 32 dake tafe.

Buni ya shaida hakan ne a yayin bikin nadin mambobin kwamitin tsare-tsare da tuntuba mai mutum 61 na jam’iyyar da suka hada da gwamnonin jam’iyyar masu ci da wasu tsofaffin gwamnoni hadi da masu ruwa da tsaki a matsayin mambobin kwamitin, bikin wanda ya gudana a sharkwatar jam’iyyar ta kasa dake Abuja.

Mai Mala yana mai karawa da cewa, jam’iyyar ta kuma tsara yadda za ta zarce wa’adi takwas a mulki.

“Manufarmu ita ce, samar da yanayin da jam’iyyar za ta zarce wa’adi 6, 7 ko 8 a karagar  mulki, domin bai wa jam’iyyar zarafin cikakkiyar damar gudanarwa da aiwatar da tsare-tsaren da take da su yadda ya kamata, na ganin ta inganta da kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya, kuma jam’iyyar ta cigaba da kasancewa jagora a Nijeriya.

“Wannan kwamitin na daga cikin dambar cimma nasarorinmu da kuma bin matakan da za su kaimu ga aiwatar da babban taron jam’iyyar.”

Ya ce, jam’iyyar wacce take da manufofi masu dumbin yawa da suke da muradin kyutata rayuwar ‘yan kasa, don haka ne ya nemi kwamitin da ya rantsar da su maida hankali wajen sauke nauyin da ke kawukansu domin tabbatar da nasarar da aka sanya a gaba.

Sannan ya shaida cewa jam’iyyar na kokarin ganin yadda za ta tafi tare da kowanne shugaba a matakai daban-daban.

What's On Your Mind?