APC Za Ta Amshi Shugabanci A Yankin Kudu-Maso-Kudu A Shekarar 2023 – Omo Agege

0
97

APC Za Ta Amshi Shugabanci A Yankin Kudu-Maso-Kudu A Shekarar 2023 – Omo Agege

Daga Yusuf Shu’aibu

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Obie Omo-Agege ya bayyana cewa, jam’iyyar APC a Jihar Delta za ta amshi ragamar shugabanci a wajen jam’iyyar PDP a shekarar 2023. Sanatan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawarsa da mataimakin shugaban ma’aikata, Barrista Aled Onwuadiamu a Illah, bayan duba aikin gyaran hanyar Asaba-Ugbolu-Illah da ke karamar hukumar Oshimili ta Arewa a cikin jihar. Omo-Agege ya bayyana cewa, yana da kwarin gwiwar cewa, jam’iyyarsa za ta amshi ragamar shugabanci a Jihar Delta da kuma dukkan jihohin da ke yankin Kudu-Maso- Kudu. Ya ce, jam’iyyarsa ta gudanar da kyakkyawan shugabanci a yankin wanda zai yi tasiri wajen zaban jam’iyyar a zaben shekarar 2023.
“Mutane su za su yi hukunci. Mu dai mun zura ido mu ga zaben shekarar 2023, wanda za a fatattaki jam’iyyar PDP a yankin gaba daya.
A cewarsa, kyakkyawan shugabancin da jam’iyyar APC wanda gwamnatin tarayya take jagoranta a Jihar Delta, shi zai janyo hankalin masu jefa kuri’a su zabi jam’iyyar.
“Bisa irin bunkasa harkokin mutane da abubuwa masu kyau da muke gudanarwa ne a yankin zai sa a zabi jam’iyyar. A yanzu idan aka ziyarci yankina, na gudanar da abubuwa masu yawa. Haka ma abokina ya gudanar a yankin Delta ta Arewa, muna gudanar da ayyukan ci gaba a yankin Kudu a wannan lokaci wadanda muka tsara abubuwa masu yawan gaske.
“Shugaban kwamitin kula da hukumar raya Neja Delta ya gabatar da ayyuka masu yawa a cikin wannan jihar. Shi ne ya gudanar da ayyukan gyaran wadannan hanyoyi dukkan su. Muna alfahari da samun sa a matsayin shugaban wannan kwamiti. Idan ya bar wannan mukami, muna cikin babban matsala wanda shi ya sa muka yi kokarin barin shi a matsayinsa. Muna murna da ayyukan da yake yi.
“Idan aka ziyarci dukkan garuruwan wannan yankuna, za a ga an kawata su da hanyoyi masu kyau a ko’ina wanda yake taimaka wa yankunan gaba daya,” in ji Sanata Omo-Agege.
Mataimakin shugaban majalisar dattijai wanda shi ke wakiltar yankin Delta ta tsakiya a majalisar dattijai ya kara da cewa, akwai bukatar bai wa sabon shugabannin tsaro dama domin gudanar da ayyuka yadda ya dace.
“Matsalar tsaro a cikin kasar nan ya shafi kowa wanda a halin yanzu yake addabar kasar nan, wanda a duk kullum ake gudanar da muhawara a zauran majalisa a kansa, ya kamata mu hada kai tare wajen magance matsalar gaba daya. Muna rokon shugaban kasa wajen ganan an samu canji a cikin shugabancin jami’an tsaro.
“An kwashe shekara da shekaru muna kira a sauya shugabannin tsaro da wasu sababbi, shugaban kasa ya ji rokonmu wanda ya canza su da sababbi a halin yanzu.
“Ina tunanin ya kamata a ba su lokaci na ganin solar zo da sababbin dubaru da za su kawo karshen rashin tsaro a cikin kasar nan,” in ji Sanata Omo-Agege.
Tun da farko dai, Barrista Onwuadiamu ya bayyana cewa, mutanen yankin Illah solar gamsu da shugabancin mataimakin shugaban majalisar dattijai wanda suke bukatar ya fito takara a zaben shekarar 2023.
“Muna bukatar canji, muna shan wahala a hannun jam’iyyar PDP. Muna neman canji wanda muna fatan samu a nan gaba kadan,” in ji shi.
Sanata Omo-Agege ya bayyana cewa, ya gamsu da ingancin aikin hanyar da hukumar kula da hanya ta tarayya take yi. Ya kara da cewa, tabbas za su kammala aikin hanyar kafin wa’adin lokacin da aka shirya.
Hanyar Asaba-Ugbolu-Ilah shi ne hanya mafi sauki da motoci suke bi daga Delta da jihohin gashin kasar nan har zuwa Abuja idan an bi ta Jihar Edo, ta dauki tsawan shekara biyu ana neman sauya ta.
Ya jaddada cewa, wakilanm mutanne daga yankin Illah solar ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja wanda suka yi masa korafi kan yanayin lalacewar hanyar tare da ganin an gyara ta.
“Tun da dai ba ni daya ba ne satana ba, ba zan iya cika musu bukatarsu ba, na sami abokina inda muka je muka sami ma’aikatar ayyuka ta tarayya. Muna gode wa shugaban kasa Buhari wanda ya amince da gyara wannan hanya, haka kuma muna mika godiyarmu ga ministan ma’aikatar ayyuka, Mista Raji Fashola,” in ji Sanata Omo-Agege.
Sanatan ya yi alkawarin zai samar da rijiyar burtsatsai masu aiki da wutar lantarki guda 500 da gina hanyoyin Otu-Umute and Otu-Onya wanda za su hada kai da Sanata Peter Nwaoboshi wanda shi ne shugaban kwamitin kula da hukumar raya Neja Delta da sanatan da ke wakiltar yankin Delta ta Arewa dukkan su za su hadu domin cika burikan mutanen wannan yankin.
Da yake gabatar da jawabi, Sanata Nwaoboshi wanda ya hada kai da Sanata Omo-Agege, ya bayyana cewa za su gudanar da wadannan ayyukan samar da rijiyar butsatsai masu aiki da wutar lantarki guda 500 da kasafin kudin shekarar 2021 ba sai har solar jira shekarar 2023 ba.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC na reshen garin Oshimili ta Arewa, Cif Ozor Njoagwuani ya yaba wa Sanata Omo-Agege bisa kokarinsa na ganin an gyara wannan hanya.

What's On Your Mind?