APC A Gombe Ta Yi Tir Da Yunkurin Bata Wa Pantami Suna

0
139

APC A Gombe Ta Yi Tir Da Yunkurin Bata Wa Pantami Suna

Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe, ta bayyana cewar yunkurin da wasu ke kan yi na ganin solar bata kima da mutuncin Ministan Sadarwa, Dakta Isah Ali Pantami abun kaico da allawadai ne, APC tana mai cewa cigaban Nijeriya ne wasu basu so don haka suke bijiro da ababen da za su dauke hankulan Ministan.

“Shugaban riko na jam’iyyar reshen Jihar Gombe, Mista Nitte Ok. Amangal, ya yi Allah wadai da gangamin da wasu marasa kishin kasa ke yi na ganin solar bata wa Ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami suna.”

Dukkanin wannan bayanin na kunshe ne ta cikin sanarwar da sakataren watsa labarai na jam’iyyar a jihar, Sabo Ibrahim ya fitar a jiya, APC tana mai cewa tabbas masu wanna yunkurin marasa kishin cigaban kasar nan ne, kuma tabbas cigaba ne ba su son gani a Nijeriya ba komai ba.

Idan za ku iya tunawa dai, a ‘yan kwanakin nan wasu solar sanya Ministan a gaba, inda suke ta kiran lallai sai ya yi murabus daga kujerarsa na Minista sakamakon samun wasu bayanan da ke nuna cewa ya taba mara wa kungiyoyin ‘yan ta’adda ba.

Da daidai lokacin da jam’iyyar take shelanta mara wa Ministan baya, ta jawo hankalinsa da kada ya tsaya biye wa irin wannan jita-jitan wasu da ke neman dauke hankalinsa daga hidimta wa kasar nan.

Dauwamammen Zaman Lafiya A Xinjiang Ya Rusa Yunkurin Wasu ‘Yan Siyasar Amurka Na Amfani Da Batun Jihar Don Hana Ci Gaban Kasar Sin

“Mun yaba wa fadar shugaban kasa da al’umman kasa masu nagarta da suka yi tsayuwar daka wajen kare Ministan daga zarge-zargen rashin hankali da wasu ke masa, wadanda ke irin wannan zarge-zargen tabbas basu nufin Nijeriya da alkairi.

“Muna tare da dan uwanmu Dakta Pantami wanda kuma mambar wannan jam’iyyar tamu mai albarka ce kana da na kwarai ga Gombe. Muna kira ga daukacin mambobin jam’iyyar nan da su yi hakan su ma domin kishin kasarmu Nijeriya.

“Muna cike da alfahari da irin nasarorin da Dakta Pantami ya cimma a matsayinsa na daga daga cikin mambobin majalisar zartaswar kasa, mun yi imanin masu yekuwar neman bata masa suna basu son ya samu nasara ne, kuma tabbas hakan bai rasa nasaba da siyasa muna da yakinin ba za su kai ga cimma nasara ba,” Inji jam’iyyar.

What's On Your Mind?