Anyi Watsi Da ‘Yan Kannywood A Taron Duniya Na Hausa Fims

0
139

Laifin Me Masana’antar Kannywood Kano Tayi Da Ba’a Gaiyace Su Bah Zuwa Taron Fim Hausa…..???

NAN ba da jimawa ba za a samar da ƙananan kwasa-kwasai a Jami’ar Bayero domin ƙara wa masu sana’ar fim ilimi, inji Shugaban Tsangayar Aikin Jarida ta jami’ar, Farfesa Mustapha Nasiru Malam.

Malamin ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar bayan  kammala taron yini biyu kan yadda ake gudanar da bincike da rubuta labaran finafinai cikin harsunan Afrika, wanda aka yi a yau a Kano.

Taron, wanda aka fi sani da ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), an gudanar da shi ne ta hanyar tsarin ga-ni-ga-ka ta manhajar Zoom.

Ɗimbin jama’a sun mahalarci taron ta hanyar Zoom

Kuma an yi shi ne tare da haɗin gwiwa tsakanin kamfanin shirya finafinai na Moving Image da ke Kano da Tsangayar Aikin Jarida ta Jami’ar Bayero, Kano (BUK).

Farfesan ya ƙara da cewa haɗin kan nasu ba zai tsaya iya shirya wannan taron ba, domin kuwa tsangayar za ta ci gaba da haɗa kai da kamfanin Moving Image, mai shirya taron na shekara-shekara, don ganin an ciyar da harkar shirya finafinai gaba. 

A nasa jawabin, shugaban Moving Image kuma jagoran shirya taron, Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana farin cikin sa ganin yadda su ka gabatar da taron a karo na uku cikin kwanciyar hankali tare da samun haɗin kan al’umma, musamman waɗanda su ka halarta.

Bugu da ƙari, ya yaba wa Tsangayar  Aikin Jarida ta BUK kan irin gudunmawar da ta bayar wajen ganin an yi taron lafiya ba tare da tangarɗar kayan aiki ba.

                   Wasu mahalarta taron

A yayin taron, an gabatar da maƙaloli kimanin 22 waɗanda su ka fito daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasar waje.

Masu gabatar da maƙalolin sun fito daga Kano, Legas, Abuja, Jamus da sauran su daga jami’o’i, kwalejojin fasaha da na iliimin aikin koyarwa.

Sai dai har zuwa lokacin kammala taron, mujallar Fim ba ta ga ‘yan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood a ciki ba duk da irin kiraye-kirayen da aka yi kan su fito su rungumi wannan tsarin domin taimaka wa cigaban sana’ar tasu.

                Lokacin gudanar da taron
Idan kun tuna, mujallar Fim ta kawo maku tattaunawar da ta yi da Alhaji Abdulkareem Muhammad a game da taron, inda ya bayyana irin ƙalubalen da su ke fuskanta kan shirya taron, musamman ƙin shiga taron da ‘yan Kannywood su ka yi.

Kada Ku Manta Zaku Iya Comments Domin Jin Ra’ayoyin Ku.

What's On Your Mind?