Ana Tuhumar Magidanci Da Lalata Kananan Yara Bakwai A Neja

0
109

Ana Tuhumar Magidanci Da Lalata Kananan Yara Bakwai A Neja

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

A makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, ta gabatar da Mista Festus Okeke dan kimanin shekaru arba’in da haihuwa gaban ‘yan jarida bisa zarginsa da yi wa kananan yara hudu fyade tare da sanya dan yatsa a gaban wasu yaran mata uku.
Festus yana zaune ne a kauyen Kurmin Giwa yana gabatar da harkokin kasuwancinsa a kauyen Ishau kusa da inda yake da zama da iyalinsa a yankin Kafin-koro cikin karamar hukumar Paikoro.
Wanda ake zargin ya bayyana cewar ya kwashe shekaru ashirin da hudu yana zama a Kurmin Giwa inda yake tafiyar da harkokin noma da kasuwanci, wanda yace shi magidanci ne yana da mata daya da ‘yaya.
Festus dai an zarge shi ne a lokacin bukin Easter na wannan shekarar yana baiwa kananan yara kudi ko buredi inda yake kai su wani karamin daki a cikin shagonsa yana lalata da su da karfi.
Yaran da rundunar ta gabatar daga kimanin ‘yan shekara goma sha uku zuwa goma ne. daya daga cikinsu da aka sakaya sunanta tace ranar bukin Easter da ya gabata ya kirani tare da kawaye na ya ba mu kyautar buredi na dari biyu, yace idan jama’a solar dauke kafa mu dawo.
Bayan mun dawo da yamma ya kira ni ya shiga da ni cikin shagon sa yace sauran su jira ba tare da bata lokaci ba ya shiga cikina, bayan ya gama yace idan na fadi zai tare ni hanyar Kurmin Giwa ya doke ni. Wadannan yaran duk ta dalilina ya samu damarsu domin a duk lokacin da muka zo zai mana alheri kuma sai ya bi daya daga cikin mu.
Yarinyar ta cigaba da cewar ko bayan mun dawo makarantar boko tunda hanyar da mu ke bi kusa da shagonsa ne, idan mun tashi tara muka zo yana ba mu lemun kwalba da buredi kyauta.
Da yake bayani a bangarensa, wanda ake zargin Mista Festus Okeke, yace maganar ba su kyautar burodi a lokacin bukin Easter ba karya ba ne.
“Yaran solar similar ni bakin shago dan ina sayar da lemun kwalba da burodi, suka ce in ba su kyautar Easter, na dauko burodin dari biyu na ba su, wannan shi ne abinda ya faru tsakani na da su.
Amma gaskiyar abinda ke faruwa shi ne, maganar shago ne. Matata na zama Ishau dan na bude mata shago can, ni kuma ina zama Kurmin Giwa ina cigaba da kasuwanci. Na karbi hayar shaguna guda biyu a nan Ishau amma saboda yanayin da ake ciki yanzu yasa ban iya zuba masu kaya duka ba.
Sai wani mutum da muke zaman mutunci da shi a nan Ishau yace yana son in ba shi aron dayan shagon, na ba shi dan lokacin ba yadda zan yi da su duka, to da na ga sauyi na bukaci ya dawo min da shagon yace ban isa ba kuma wani tunzurin da zan yi na karban shagon yana iya jefa ni inda ban yi tsammani ba, domin solar fara ajiyar wake a cikin shagon.
Ranar lahadin nan ina Kurmin Giwa sai wani dan kabilar mu da ake cewar Pepe yace min hakimi na kira na, na kokarin sanin abinda yake faruwa daga wajensa yaki bayyana min komai.
Bayan na isa wajen hakimin na tarar mutane solar hadu a zauren, na shiga kamar yadda aka saba idan an kira taro sai aka umurci in fita. Zuwa wani lokaci ba kira ba tunda na dauko ‘yayana ne zan kai su shago, sai na tafi dan kai su daga baya sai in dawo, mun kusa isa wajen sai na ga mutane suna fasa shagona.
Lokacin na yi kokarin isa wajen, sai wata dattijiya ‘yar kabilar mu ta umurci in bar wajen in tafi in sanar da ‘yan sanda. Bayan na samu tsaro daga wajen ‘yan sandan Moppal, a lokacin ne na ji wai mutanen suna zargina da yiwa kananan yara bakwai fyade.
Wasiu A. Abiodun, shi ne jami’in hulda da manema labarai, yace rundunar su za ta cigaba da bin kadin batun dan sanin hakikanin abinda ke faruwa.
Yanzu dai yara hudu solar tabbatar mana wanda ake zargin yayi masu fyade yayin da uku suka ce ya sanya masu yatsa a gaban su.
Za mu tabbatar mun kammala bincike cikin lokaci dan gabatar da batun gaban kuliya, in ji shi.

What's On Your Mind?