Ana Shirin Kafa Dokar Daure Masu Biyan Kudin Fansa Shekara 15 A Nijeriya

- Advertisement -

Ana Shirin Kafa Dokar Daure Masu Biyan Kudin Fansa Shekara 15 A Nijeriya

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

Majalisar Dattawa ta gabatar da kudirin dokar daurin shekaru 15 ga duk wani dan Nijeriya da ya biya kudin fansa ga masu satar mutane.

A ranar Laraba ce Majalisar ta yi la’akari da wani kudurin doka da ke neman hana biya da karbar kudin fansa don sakin duk wani mutum da aka sace, ko aka daure shi, ko aka tsare shi bisa kuskure.
Mai taimaka wa shugaban majalisar, Ahmed Lawan a kan harkokin yada labarai, Ezrel Tabiowo, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya kara da cewa Dokar Rigakafin Ta’addanci da aka yi wa Kwaskwarima ta 2021, wacce ta tsallaka karatu na biyu, Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya dauki nauyin gabatarwa.
Da yake jagorantar muhawara kan kudurin, dan majalisar ya ce, dokar tana neman gyara dokar ta’addanci ta 2013 ne don haramta biyan kudin fansa ga masu satar mutane, da ‘yan ta’adda don sakin duk wani wanda aka tsare ko daure ko sacewa bisa kuskure.
A cewar Onyewuchi, kudirin dokar na neman maye gurbin sashi na 14 na Babbar Dokar a wani sabon sashi da ya kunshi bayanin: “Duk wanda ya tura kudade, ya biya ko kuma ya hada baki da wani mai satar mutane ko kuma dan ta’adda don karbar duk wani fansa don sakin kowane mutum wanda aka tsare bisa kuskure, ko aka saka shi a kurkuku ko kuma aka sace shi, to ya aikata babban laifi kuma yana iya fuskantar hukuncin dauri a gidan yari na akalla shekaru 15. ”
Ya kara da cewa, satar mutane ta zama kasuwanci mai saurin kawo kudi mai yawa a kasar nan, “yanzu haka garkuwa da mutane ya kasance mafi munin ayyukan ‘yan ta’adda a Nijeriya kuma mafi munin ta’addanci da ake fuskanta a kasar.”
Da yake danganta yawaitar sace-sacen mutane a kasar ga dalilai kamar su cin hanci da rashawa, rashin aikin yi, talauci da hadin gwiwar jami’an tsaro, Onyewuchi ya koka kan yadda yawaitar yin garkuwa da mutane a kullum ke jefa mafi yawan ‘Yan Nijeriya cikin hadari.
“Satar mutane na karuwa a Nijeriya kuma ya zama ruwan dare a dukkan shiyyoyin siyasa.
“Wadansu suna zargin hauhawar wannan aika-aika a kan talauci, addini, siyasa, karancin dokokin da ake da su, rashin aikin yi, hadin gwiwar jami’an tsaro, cin hanci da rashawa, da son kai a tsakanin wasu.
“Matasanmu marasa aikin yi su ma solar koma satar mutane don neman kudi (fansa) a matsayin dabarun rayuwa.
“Ko ma dai wane dalili ne, a bayyane yake cewa satar mutane a Nijeriya na jefa kowa a cikin hadari, attajirai da matalauta, tsofaffi da samari, maza da mata, baki, sarakunan gargajiya da shugabannin addini da sauransu. ”In ji shi.
Da yake tsokaci sport da rahoton da jaridar Monetary Occasions da USA World Danger Consultancy suka hada a watan Nuwamba, 2019, dan majalisar ya lura cewa Nijeriya ta fi kowacce yawan masu satar mutane don neman kudin fansa na ‘yan gida da kuma baki a duk Afirka saboda suna aika-aikar a kowace daga cikin jihohin kasar 36 .
Ya lura cewa kasashe kamar Amurka da Ingila ba sa goyon bayan biyan kudin fansa ga masu satar mutane.
“Biyan kudaden fansa na ‘yan ta’adda haramtacce ne a karkashin Dokar Ta’addanci ta Burtaniya ta 2000 yayin da Amurka ke bin wata ka’ida ta a kan biyan kudin fansa,” in ji Mista Onyewuchi
Ya ba da shawarar cewa, “bai kamata a karfafa ci gaba da biyan kudin fansa, baya ga haka ya kamata gwamnati ta samar da isasshen tsaro da karfafa tattalin arziki cikin gaggawa, ta hanzarta shirye-shiryenta na kawar da talauci, samar da ayyukan yi ga matasa wadanda galibi ke cikin mummunar sana’ar satar mutane don kawo karshen matsalar. ”
Bayan kammala karatu na biyu na kudirin Dokar Rigakafin Ta’addanci da ake wa Kwaskwarima ta 2021, sai Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya mika shi ga Kwamitin Kula da Harkokin Shari’a, ‘Yancin dan Adam don ci gaba da aiki a kan dokar.
Kwamitin bisa jagorancin Sanata Micheal Opeyemi Bamidele ana sa rai ya bayar da rahotonsa cikin makwanni hudu.

- Advertisement -