Ana sauran sa’o’i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa

0
188

Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa

Mutuwar wani dan Najeriya kasa da sa’o’i biyu kafin bikin auren shi ya gigita jama’ar yankin Ikyangedu dake jihar Nasarawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mota ce ta bige angon mai suna John Abugu yayin da yaje karbo rigar da zai saka wurin daurin auren daga shagon mai wanki da guga.

Amarya mai suna Rosemary Hudu, ‘yar kasuwa ce wacce ta fada tsananin jimami bayan jin labarin mutuwar ango Abugu.

A yayin bayyana damuwarta, Rosemary tace ta so a ce mutuwa tayi tare da angonata.

Ta ce: “Na so a ce nima na mutu ta yadda za a birnemu tare. Har yanzu ban yadda ba cewa mijina ya mutu ana sauran sa’o’i kadan daura aurenmu. Ba zan iya cewa komai ba, amma duk inda yake zan kasance tare dashi.”

Wani abokin marigayin ango mai suna Julius, yace yana tare da mamacin lokacin da hatsarin ya faru a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilun 2021.

Da duminsa: Bayan sa’o’i kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno

Yayin bada labarin yadda lamarin mai matukar firgitarwa ya faru, ya ce: ” Da yaso zuwa wurin mai wanki da guga, na ce zan tuka babur din amma sai yace kada in damu zai tuka.

“Yana bani labarin wani abokinsa da zai zo ya kaisu wurin bikin da motar angon kuma ya mayar dasu gida bayan bikin. Saboda farin cikin dake tare da shi, bai kalla ko ina ba kawai ya shiga babbar hanyar inda mota kirar Hilux tayi ciki damu.

“Tuni aka gaggauta mika mu asibiti kuma aka fara bamu taimakon likitoci. Ko a asibitin, tare ake duba mu. Amma bayan mintuna kadan, lamarin shi ya kara kamari inda ya fara zubda jini ta ido, hanci da kunne kuma ya mutu.”

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja yayi karya da yace gwamnonin PDP na arewacin Najeriya sune suka kayar dashi a 2015 ta hanyar hade masa kai.

A ranar Juma’a, Aliyu yace gwamnonin PDP na jihohin arewacin Najeriya solar soki bukatarsa ta zarcewa bayan ya ki cika alkawarinsa na hakura da mulki a wa’adin farko.

“Tunda hakan ya ci karo da yarjejeniyarmu ta farko a jam’iyyar, kuma mu gwamnonin arewa muke ganin za a cuce mu idan Jonathan yayi nasara, sai muka tashi muka hana hakan faruwa,” yace.

Supply: Legit

What's On Your Mind?