Ana Kara Gano Fuska Biyu Da Amurka Take Nunawa Kan Batun Hakkin Dan Adam

- Advertisement -

Ana Kara Gano Fuska Biyu Da Amurka Take Nunawa Kan Batun Hakkin Dan Adam

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, ana ta kara gano fuska biyu da kasar Amurka take nunawa, kan batun da ya shafi hakkin dan Adam.

Tashar intanet ta “Africa-China Assessment”, ta wallafa wani bayani mai taken “Me ya sa kasashen Afirka suka goyi bayan China, amma suka ki yarda da kasashen yamma kan batun hakkin dan Adam”, inda a ciki aka nuna cewa, zargin da kasashen yamman suka yiwa kasar Sin, na cewa wai tana “kisan kare-dangi”, da tilastawa ma’aikata aiki a Xinjiang, babbar karya ce zalla, kuma ainihin makasudin su shi ne tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da hana ci gaban kasar.

Bayanin ya kuma ce, kasashen da suka zargi kasar Sin, su ne suka aikata munanan laifuffuka a fannin keta hakkin ‘yan asalin Afirka, don haka ba su cancanci su soki lamarin sauran kasashe ba. Kaza lika kasashen Afirka suna goyon-bayan kasar Sin kan batun hakkin dan Adam, saboda Afirka da Sin duk solar taba jin radadi a jikinsu, na irin yanayin da kasashen yamma suka haifar musu.

Madam Hua ta yi karin haske da cewa, a hakikanin gaskiya, ana kara samun kasashe, ciki har da na Afirka, wadanda suke kara fahimtar makircin Amurka, da na sauran wasu kasashen yamma, sport da yunkurin hana ci gaban kasar Sin, bisa hujjar kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

 

- Advertisement -