… Ana Ci Gaba Da Zaman Dar-dar A Gaidam 

0
163

… Ana Ci Gaba Da Zaman Dar-dar A Gaidam 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Gaidam ta jihar Yobe, sakamakon dirar mikiya da mayakan ISWAP masu fafutikar kafa daula a yammacin Afrika suka yi wa garin a motoci kirar Hilud sama da 20, tare da ci gaba da kasancewa a garin tun ranar Jummu’a, wanda hakan ya tilasta wa jama’a kaura domin tsira da rayukansu zuwa wasu garuruwa a ciki da wajen jihar.

Wani da abin ya rusa da shi, Modu Fannami ya ce, “Wallahi ba domin na yi aure ba, ni da Gaidam a kalla sai bayan shekaru goma masu zuwa, Saboda yadda mun ga tashin hankalin da ba zai misaltu ba. Musamman a lokaci makamancin wannan, ga kishirwar azumi ga firgici a lokacin da boko haram ke ruwan wuta a garin babu kakkauta wa.”

“Sannan babban abin damuwa, harin ya zo a cikin mawuyacin hali, wasu da dama basu da abincin da zasu ci balle kudin mota; saboda haka ne ya jawo wasu da dama a kafa suke kana ba tare da sanin inda suka nufa ba. Sannan ga yara da mata tare da tsuffi, ga tashin hankali kuma babu wani tallafi.” In ji shi.

Wakilinmu ya ziyarci gefen yankin domin ganin yadda al’amarin yake, inda ya fara da yada zango a garin Bayamari- mahadar hanyoyin da suka fito daga Damaturu, Gashuwa da Gaidam a jihar Yobe. Wanda daruruwan yan hijirar da suka yi cirko-cirko kafin yanke shawarar garuruwan da za su tunkara, wadanda suka kunshi yara da matsakaita da tsuffi- maza da mata, cike da alamar damuwa a fuskokinsu.

Jama’a da dama wadanda wakilinmu ya ci karo dasu a yankin, solar shaidar da cewa har yanzu akwai sauran zaman dar-dar a garin, tare da bayyana fargabar mayakan suna ci gaba da mamaye Gaidam. “Ko a jiya da secure na hango boko haram suna bi gida-gida, suna yi wa mutane wa’azi. Suna kokarin bamu hakuri da gaya mana cewa duk mai son zama ya ci gaba da zamansa, ba su zo da niyyar fira ba.”

“Har ila yau, za ka ga suna yawo a gari, da dare kuma su kafa gidan sauro; su yi baccinsu bayan dafa shayi, abinci da sauran harkokin su. Baya ga kashen mutane, kona dukiyoyin jama’a bila adadin. A ranar Asabar, bam ya halaka mutum 11 a gida guda- a Gaidam a sa’ilin da jirgin yaki ya yi kokarin auna yan ta’addan, wanda ranar Lahadi aka yi jana’izar gawawakin su a Damaturu.

Bugu da kari kuma, `yan ta’addan solar katse cibiyoyin sadarwa na kamfanonin Airtel da MTN ta hanyar banka musu wuta tare da wawushe kayan abinci da na masarufi a shagunan jama’a.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban karamar hukumar Gaidam, Ali Kolo Gaidam, ta hanyar wayar tafi-da-gidanka, ya tabbatar da cewa dubun-dubatar jama’ar sa solar kauracewa garin.”

“Yanzu haka ban san waye ke da iko da garin ba, saboda yau kimanin kwana biyu da suka wuce na kasa shiga garin, amma bisa bayanan da nake samu shi ne mayakan solar fi karfin sojojin da ke aikin tsaro a garin.”

“Har wala yau kuma, na samu damar ziyartar wadanda suka samu raunuka a harin, wadanda aka kwantar a asibitin kwararru dake Damaturu tare da jajenta musu dangane da halin da suka shiga.” Ta bakin shi.

Haka kuma, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa yan ta’addan solar yi wa mutum biyu yankan rago- wanda suka hada da malamin makaranta a Kawuri Major Faculty, da Mallam Baba Tazira baya ga wadanda suka samu mabambantan raunuka. Kana kuma ya musanta ikirarin sojoji dangane da batun kashe wasu mahara a garin.

What's On Your Mind?