Ana Ci Gaba Da Gasar Karatun Alkur’ani A Kano

0
141

Ana Ci Gaba Da Gasar Karatun Alkur’ani A Kano

Dukkan jihohi 36 na tarayyar kasar nan da yankin babbar birnin tarayya Abuja ke fafatawa a gasar musabakar karatun al’kurani mai girna na kasa karo na 35 da ke gudana a halin yanzu a garin Kanon dabo, wadda aka fara ranar Juma’a.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar a jawabinsa ya lura da cewa, Nijeriya ta halarci gasar karatun kurani na kasa da kasa a karo da dama a lokuttan baya.

Mai alfarmar ya samu wakilcin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ne, ya kuma bayyana ne cewa, taron a mastayin mai lada sosai.

Ya kuma bukaci masu shiga gasar su natsu don su samu nasarar da ya kamata, ya kuma gargadi alkalan gasar su ji tsoron Allah a yayin gudanar da yyukansu na yanke hukunci a gasar.

Ya kuma ce, an samu nasarorin gudanar da gasar ne a lokuttan baya saboda yadda masu ruwa da tsaki suka jajirce wajen sauke nauyin su tun daga matakin karamar hukuma zuwa gwamnatin tarayya.

Sarkin Muslmi ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano akan yadda ta samar da hukumar kula da almajirai da makaratun islamiyoyi a jihar don tabbatra da cimma makasudin assasa bangarorin gaba daya.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da ilimi kyauta kuma dole ga dukkan al’ummar jihar ta kuma shirya sake fasalin tsarin almajiranci a jihar.

Ɗan Najeraya mai shekaru 23 ya zo na ɗaya a gasar Al-Qur’ani ta duniya a ƙasar Kenya

Ya kuma wannan shi ne karo na uku da jihar Kano ke daukar nauyin gasar ta kuma kasance zakara a lokutta da dama, ya ce gwmanatinsa tana mahimantar da harkar karatun addini.

Shugaban kwamitin shirya musabakar, kuma shugaban jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Usman Lawal, ya ce, gasar zai fito da wadanda za su wakilci Nijeriya a gasar da za a gudanar a fagen kasa da kasa a nan gaba.

Haka kuma gasar zai kara dakon zumunci da soyyaya a tsakanin matasa musulmi na fadin kasar nan kamar yadda al’kur’ani da hadisi suka karantar da mu ” inji shi.

What's On Your Mind?