An Yi Taron Karawa Juna Sani Mai Taken “Xinjiang Kyakkyawan Wuri Ne” A Urumqi

- Advertisement -

An Yi Taron Karawa Juna Sani Mai Taken “Xinjiang Kyakkyawan Wuri Ne” A Urumqi

Daga CRI Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin gami da gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar solar gudanar da taron karawa juna sani mai taken “Xinjiang kyakkyawan wuri ne” a birnin Urumqi, inda wasu jakadun kasashen nahiyar Latin Amurka da Caribbean dake kasar Sin su 23 suka halarci taron.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng ya bayyana cewa, makasudin gayyatar jakadun kasashe daban-daban don su ziyarci Xinjiang a wannan karo shi ne, domin samar musu da damammakin tuntubar al’ummomin jihar, da ganewa idanunsu yadda ake samun ci gaba da kwanciyar hankali a wurin.

A wajen taron, jakadun kasashen Uruguay da Ecuador da Brazil da Cuba da Bahamas solar bayyana cewa, ta hanyar ziyarar gani da ido, solar kara fahimtar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Xinjiang, gami da yadda tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma ke bunkasa a wajen, da kuma nasarorin da aka samu wajen tabbatar da ‘yancin bin addini da kyautata rayuwar al’umma a jihar. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

- Advertisement -