An yi ram da wani wanda yake kawowa Mayakan Boko Haram asirin Sojoji inji DHQ

0
151

An yi ram da wani wanda yake kawowa Mayakan Boko Haram asirin Sojoji inji DHQ

Sojojin Najeriya solar ce dakarun Operation Lafiya Dole solar yi ram da wani da ake zargin ‘dan Boko Haram ne da yake yi masu leken asiri.

Kamar yadda gidan sojan ya bayyana, wannan mutumi ya na tattara sirrin dakarun Najeriya, ya je ya fa fada wa mayakan kungiyar Boko Haram.

Ana zargin cewa wannan mutumi ne ya yi sanadiyyar wani mummunan harin da ‘yan ta’addan su ka kai wa sojoji a yankin Kamuya, jihar Yobe.

Sanarwar da aka fitar ya ce darektan yada labaran sojojin kasa, Birgediya Janar Mohammed M. Yerima ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Da yake magana a jiya ranar Lahadi, 18 ga watan Afrilu, 2021, Janar Mohammed M. Yerima ya bada sunan wannan mutumi a matsayin Modu Ari.

Juna-biyu Ta Yi Kundunbala Cikin Ruwa Don Ceto Mijinta

Mai magana da yawun sojojin ya ce Modu Ari ya fada hannun dakarun 27 Activity Drive Brigade, inda ya amsa cewa ya na bibiyar sojojin Najeriya.

Ari ya na bin sahun sojoji, daga nan kuma sai ya kai wa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram labari.

Kama wannan mutumi da aka yi ya sa rundunar sojojin kasar ta shiga bin diddiki domin cafke duk wadanda su ke yi wa ‘Yan Boko Haram leken asiri.

Jami’in ya ce: Ana bincike domin bankado sauran mutanen gari da ake hada baki da su ana samun sirrin sojoji, wanda hakan ke jefa jami’ai a cikin hadari.”

A cewar darektan yada labaran, leken asirin da ake yi wa sojoji a bangaren Timbuktu, ya jawo cikas.

A jiya aka ji cewa Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) da manyan hafsoshin tsaro solar kai ziyara zuwa garin Maiduguri, jihar Borno.

Ministan ya samu rakiyar Janar Fortunate Irabor tare da sauran hafsoshin sojoji na kasa, inda su ka duba yanayin barnar da ‘yan Boko Haram suka yi a jihar.

Supply: Legit

What's On Your Mind?