HOTUNA: An yi jana’izar marigayi Alhaji Balarabe Musa a Kaduna

- Advertisement -

An jana’izar tsohon gwamnan Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa a Ungwan Sarki Kaduna

Cikin wadanda suka hallarci jana’izar akwai Sanata Shehu Sani da tsaffin gwamnonin Kaduna, Ramalan Yero, Ahmed Makarfi

Marigayin ya rasu yana da shekaru 84 a duniya ya kuma bar yara da jikoki An yau Laraba 11 ga watan Nuwamba ne aka yi jana’izar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a garin Kaduna.

Ya rasu sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Laraba yana a gidansa ke Ungwan Sarki a Kaduna.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 84 a duniya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An yi jana'izar marigayi Alhaji Balarabe Musa a Kaduna

An yi jana'izar marigayi Alhaji Balarabe Musa a Kaduna

An yi jana’izarsa a maƙabartar Ungwan Sarki misalin ƙarfe 5 bayan an sama salla a masallacin Sultan Bello da ke Ungwan Sarki a Kaduna.

Ungwan Sarki na karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ne a jihar.

Manyan mutane da ƴan siyasa dama solar hallarci jana’izar ciki har da tsaffin gwamnonin jihar Kaduna Ramalan Yero da Ahmed Makarfi.

AN YANKA TA TASHI: Matar Aure Dauda Kahutu Rarara Ya Saka A Matsayin Jarumar Wakar Jahata Ce

Saura solar haɗa da Babban Alƙalin Jihar Kaduna, Mai Shari’a Mohammed Lawal, ɗan takarar gwamnan PDP a zaben 2019, Hon Ishah Mohammed Ashiru da kwamishinoni da hakimai.

Gwamna Nasiru El-Rufai bai samu hallartar jana’izar ba domin baya kasar amma sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas Lawal ya wakilce shi.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin, Kazeem ya ce zai rika tuna mahaifinsa a matsayin “mutum mai ƙaunar talakawa kuma ya bani tarbiyya tare da koyar da nirayuwar duniya.

Ina kuma son irin siyasarsa. “Mutum ne mai gaskiya kuma baya ɓoye-ɓoye.”

A wani labarin, An samu rashin jituwa tsakanin mambobin kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan ‘yan gudun hijira a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin Ma’aikatar JinKai da Kare Bala’i.

The Channels television ta ruwaito wani dan majalisa, Fatuhu Muhammad ya fice daga zaman kwamitin majalisar yayin da ministan ma’aikatar Jin Kai, Sadiya Umar Farouk ke kare kasafin kudin ma’aikatar ta.

- Advertisement -