An Yi Idin Karamar Sallah A Masallacin Birnin Tulufan Na Xinjiang

- Advertisement -

An Yi Idin Karamar Sallah A Masallacin Birnin Tulufan Na Xinjiang

Daga CRI Hausa

A jiya ne, al’ummar musulman yankin Gaochang na birnin Tulufan dake jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin, suka yi Idim karamar sallah a masallacin Medris, wanda ke da tsawon tarihin shekaru 350, inda suka karanta ayoyin Alkura’ani.

Jiya ne, daukacin musulman kasashen duniya suka yi bikin karamar sallah, a wannan rana da sanyin safiya, al’ummar musulmai na kabilu daban daban dake zaune a unguwar Huoyanshan ta garin Putao na yankin Gaochang na birnin Tulufan dake jihar Xinjiang solar isa masallacin Medris dake kusa da unguwarsu, domin halartar Idin karamar sallah.

Limamin masallacin Ahmat Abdulla ya bayyana cewa, musulmai wadanda za su zo masallacin yin sallah za su karu matuka da bikin, a don haka solar shirya sosai a masallacin, yana mai cewa, “Musulmai da suka zo masallacin yin sallah suna da yawan gaske, ma’aikatan masallacinmu suna auna zafin jikinsu, kuma solar ba su sinadarin kashe kwayoyin cuta, ta yadda za a gudanar da Idin karamar sallah lami lafiya.”
A masallacin, wakilinmu ya ga musulmai masu yawan gaske suna zaune a ciki, kowanensu ya sa kayan kabilarsa, tare kuma da sanya marufin baki da hanci, haka kuma solar ba da tazarar mita daya a tsakanin juna kamar yadda aka zana alamomi a tsakanin shimfidar da suke zaune.

Duk da cewa, ba a iya ganin fuskarsu, amma za a fahimci cewa, kowa yana murnar wannan rana daga gaisuwar da suke yiwa juna.

Kaka Yasin Keram, wanda ya sa hula mai hoton furanni ya bayyana cewa, “Dokokin da aka sanya a masallacin suna da kyau kwarai, ina jin dadin sallah matuka yau.”
Musulmai suna ta tayar da kabbara, kowa ya tashi tsayi, solar fara yin sallah, suna kuma sauraron ayoyin Alkura’anin da limamin yake karantawa.

Bayan idar da sallah, musulmai solar fita daga masallacin, solar je kasuwa dake kusa domin sayen nama da kayan lambu da kuma ‘ya’yan itatuwa.

Batur Tursun, ‘dan kabilar Uygur yana zaune ne a unguwar dake kusa da kasuwar, ya gaya mana cewa, yau yaransa za su koma gida daga birnin Urumqi, fadar jihar Xinjiang domin murnar bikin karamar sallah tare da su, a cewarsa: “Tun jiya, Ni da matata mun riga mun sayi naman tunkiya da na saniya da kayayyakin lambu da ‘ya’yan itatuwa a kasuwa, yau yaranmu da jikokinmu za su koma gida domin murnar bikin karamar sallah tare da mu, gaba daya akwai mutane 12 a babban iyalinmu, muna farin ciki sosai.”(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

- Advertisement -