An Yaba Wa Gwamnatin Nijeriya Kan Shirinta Na Dawo Da Martabar Noma

0
13

An yaba wa gwamnatin tarayyar Najeriya kan dawo da martabar noma kasar nan, domin hakan zai taimaka wajen jama’ar samun ayyukan yi a lokacin damuna da kuma rani, wanda ita kan ta kasar zai taimake ta wajen hana shigo da abinci daga kasashen duniya.

Malam Garba Abubakar dahiru wani manomi ne yayi yabon lokacin da yake bayyana ra’ayinsa kan shirin gwamnati na baiwa babban bakin Najeriya na shiga cikin harkokin noma ka’in da na’in da ita kan ta babban bankin zai taimaka ma ta wajen samun kudaden shiga daga hannun ‘yan kasa mai makon dogaro da man fetur da kan janyowa tattalin arzikin kasa koma bayan yadda kasuwar sa ya koma baya a duniya.

An Yaba Wa Gwamnatin Nijeriya Kan Shirinta Na Dawo Da Martabar Noma

Yanzu haka shirin baiwa manoma tallafin babban bankin yayi nisa musamman akan noman masara, shinkafa, alkama, auduga da tumatur wanda hakan zai taimaka wajen samun yalwar abinci a kasar nan da talaka ke kokawa akan shi yau. Idan har shirin noman damana da na rani zai cigaba a haka nan gaba za mu dara sosai ta yadda za mu yaki yunwa da rashin aikin yi ga jama’a cikin sauki.

Malamin ya cigaba da cewar idan abinci ya yalwata ina da tabbacin za a iya samun kananan kamfanoni da za su taso dan shiga kasuwannin duniya, yau mun ga illar watsi da noma da mu ka yi sanadiyar annobar Korona, da ya sanya aka rufe iyakokin kasa, da tun farko ba mu yi watsi da noma ba da irin wahalhalun da muke fuskan na tsadar abinci bai ta so ba, ita kan ta kasar da ta samu matsin tattalin arziki da ta ke fuskan ta yanzu ba.

Tabbas gwamnatocin da suka gabata ba su taimaka ba, amma tunda zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tada mu dogon baccin da mu ka yi a baya, Allah yasa gwamnatocin da zasu gaje ta su cigaba da tafiyar da wannan shirin.

Gurguwa Da Auren Nesa: Bayan Titin Kano-Kaduna-Abuja Ya Gagari Kundila..?

Duk abinda aka bari kuma aka ga illar barinsa idan aka ce za a dawo kan sa sai an fuskanci matsaloli, ya kamata ‘yan Najeriya su marawa gwamnati baya wajen ganin wannan kudurin ya cigaba. Domin watsi da mu ka yi da tarihin mu na baya da ya taimaka wajen kafuwar tattalin arzikin kasar nan, aka mayar da hankali akan abinda noman ya haifar yasa rayuwa ta ke yiwa al’umma tsada a yau.

Ya kamata wadanda suka ci gajiyar shirin kar su sakacin da zai sa a koma inda aka fito, dole ne duk wanda aka tallafawa ya tabbatar ya sarrafa abin nan yadda ya dace. Mafi yawan lokutta a lokacin da aka shiga tsanani akan dawo akan tunanin mafita, wanda bayan fita daga cikin matsin kuma sai a manta da wahalhakun da aka fito.

Malam Garba yace akwai wani hanzari ba gudu ba da yake ciwa manoma tuwo a kwarya, shi ne matsalar tsaro na ‘yan bindiga masu garkuwa da jama’a musamman a jihar Neja. Lallai gwamnati da jami’an tsaro na bakin kokarinsu mu na gani, amma akwai bukatar gwamnatin da jami’an tsaro su kara kaimi domin mafi yawan manoman ‘yan bindiga photo voltaic koro su daga matsugunnan su, wanda in har ba a dauki kwakkwaran matakan da suka da ce ba za a cigaba da daura zani yana kwancewa a kasuwa.

Ya kamata kamar yadda jami’an tsaro suke kokawa akan hakkokan su da rashin wadatattun kayan aiki, gwamnati ta kokarta wajen samar masu da abubuwan da suka da ce. Misalin jami’an tsaron farin kaya na kokarin samo bayanin duk wani abinda zai faru, to a karfafa masu guiwa wajen daukar matakan hana faruwar abin.

Su kan su sojoji da ‘yan sanda har ‘yan sintiri suna bukatar kulawa yadda ya dace, domin ba ka tura mutum ya tsare jama’a daga hareharen batagari alhalin ba kai mai tanadin abinda ya ke bukata ba, saboda yadda rahotanni ke zuwa batagarin nan na anfani da makaman da yafi na jami’an tsaron mu, mai makon suna shiga ana kashe su ya kamata a samar masu kayan kariya ta yadda za su iya cin galabar batagarin.

Da ya juya kan sauran jama’a kuwa, Malam Garba yace akwai bukatar yin aiki kafada da kafada da jami’an tsaro wajen tsengunta masu duk wani makircin makiya zaman lafiya a kasar nan. Ga shirin gwamnati na tsaron al’umma a hannun su, to su yi anfani da wannan damar wajen kai rahoton duk wani yunkuri na yiwa zaman lafiyar kasan zagon kasa da batagarin, hakan zai taimaka ainun wajen baiwa jami’an tsaro kwarin guiwa ta yadda za su iya dakushe faruwar duk wata barna.

What's On Your Mind?