An tsinci gawarwakin sojoji 11 da ‘yan bindiga suka kaiwa hari a Benue

0
139

An tsinci gawarwakin sojoji 11 da 'yan bindiga suka kaiwa hari a Benue

Rundunar sojojin Nigeria ta sanar da rasuwar sojoji 11 a jihar Benue

Wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kaiwa sojojin hari a Konshisha

Da farko an sanar da sojojin solar bace amma daga bisani an tsinci gawarwakinsu

Rundunar ta ce an fara bincike gadan-gadan da nufin kamo wadanda suka yi laifin

Wasu da ake zargin yan bindiga ne solar kashe jami’in soja daya da dakarun sojoji 10 a jihar Benue a yayin da suka fita aiki kamar yadda rundunar Sojin Nigeria ta sanar.

Kakakin rundunar soji, Janar Mohammed Yerima ya ce da farko an ce sojojin solar bace amma daga bisani an gano gawarwakinsu a karamar hukumar Konshisha na jihar a sakon da ya fitar daren ranar Alhamis a shafinta na Twitter.

An ceto wasu daga matasan takum 25 da aka sace

“Da farko an bada sanarwar bacewar sojojin ne da suka kunshi jami’i daya da dakaru 10 hakan yasa aka aike da tawagar masu bincike da ceto da ta kunshi sojojin da jami’an Operation Whirl Stroke.

“Tawagar da ke nemansu, ta gano gawarwakin dukkan sojojin 10 a karamar hukumar Konshisha a jihar Benue,” wani sashi na sanarwar.

Fittatun Farfesoshin Nigeria 13 da suka rasu a 2020

Sanarwar ta kara da cewa an kwashe gawarwarkin nan take sannan ana cigaba da bincike da nufin gano wadanda suka aikata wannan mummunan lamarin da nufin hukunta su.

Yerima ya ce babban hafsan sojojin kasa ya umurci kwamandojin da ke aiki su tabbatar an gano wadanda suka aikata wannan laifin domin su dandana kudarsu.

Rundunar Sojin ta yi kira ga mutane su taimaka mata da bayanai masu amfani da za su taimaka a kama wadanda suka kai wannan harin.

Tunda farko kun ji cewa, ‘yan bindiga solar kwace makamai masu yawa da zunzurutun kudi Naira miliyan 28 daga hannun wata ayarin motocin sojoji da suka afka wa a jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

Sojojin solar fito ne daga karamar hukumar Katsina-Ala suna hanyarsu na zuwa karamar hukumar Oju (mai nisan kilomita 171 daga Katsina-Ala) yayin da yan bindigan suka tare su a Konshisha a ranar Talata, wata majiya ta shaidawa The Gazette.

Twitter Wani babban jami’in soja ya ce yan bindigan da suka kai wa sojojin hari solar kwace makamai da kudi N28m suka tsere da su a tsakar daren suka bi hanyar gabar rafin Benue.

Supply: Legit.ng

What's On Your Mind?