An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir’aun Tieta, shekara 2,500 baya

A ranar Asabar ne kasar Misra, wacce yanzu ake kira ‘Egypt’, ta sanar da cewa wasu masu binciken ma’adanan karkashin kasa solar bankado wani tsohon tarihi a Saqqara da ke kudancin Cairo.

Masu binciken solar gano wata makabarta a karkashin kasa wacce fitaccen masanin tarihin Egypt, Zahi Hawass, ya ce an ginata ne a matsayin wurin binne Sarauniya Naert, kamar yadda Channels ta rawaito.

Sarauniya Naert mata ce wurin Fir’auna Teti, Sarki na farko a gidan masarauta ta 6 da ta mulki kasar Misra.

Ita kanta makabarta an gano ta ne daura da ginin tsibirin da aka binne shi kansa Fir’auna Teti a karni na 11 kafin zuwan Annabi Isa (BC).

An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya

A cewar Hawass, gano makabartar zai cike wani gurbin tarihi da aka dade ana nema domin fahimtar alakar tsakanin wasu al’amura na karni 16 da na karni 11 kafin zuwan Annabi Isa.

An gano wasu akwatunan katako da kuma wasu kaya da kaya da aka sassaka da itace wanda binciken kimiyya ya gano cewa an kera su fiye da shekaru 2,500 da suka gabata.

An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya

Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

A cikin akwatinan, wadanda aka binne a ramuka fiye da hamsin, akwai gawa dauke da wasu kaya da suka hada da litattafai da makaman yaki.

Sauran kayan da aka samu solar hada da fuskoki da aka sassaka daga itace, kwale-kwale da takaitaccen rubutu a jikinsa da aka tsakuro daga wani littafi da aka bayyana da ‘littafin mutuwa’.

Kayayyakin solar nuna alamar cewa gawarwakin sojoji ne irin na tsohuwar masarautar Misra mai dumbin tarihi.

A kwanakin baya ne ministan gargajiya da bunkasa harkokin bude ido a kasar Egypt, Khaled al-Anani, ya sanar da cewa da sauran abubuwan tarihi da za’a iya cigaba da ganowa a Saqqara.

Legit.ng ta taba wallafa cewa Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su.

Akwai ɗumbin kayan tarihi da ake samu a Santambul da ba kasafai ake samunsu daga sauran sassan duniyar da Musulunci ya mulka a baya ba.

Shahararren malamin addinin Islama a arewacin Nigeria, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyanawa gidan labarai na BBC dalilin da yasa ake jingina Annabi da kayan tarihi da aka samu a Turkiyya.

 711 total views,  5 views today

About M. Jamiu 1373 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*