An Siffata Mutane Cikin Zunubi 

0
70

An Siffata Mutane Cikin Zunubi 

“Gashi, chikin migunta aka sifanta ni, cikun zunubi kuma uwata ta dauki chikinsa” (Zabura 51:1).

“Babban magana wai mahaukaci ya hau kura”. Na fara da wannan Karin maganan ne, domin in mun dauki lokaci muka dubi halin dan’adam, to za mu gane da dalilin da na fara da karin maganan. Wani mawakin Hausa watau Alhaji Danmaraya Jos, ya yi waka da cewa “Dan’adam mai wuya gane hali.”

Ashe, wannan wakar na tafiya daidai da wannan ayar. Mai Zabura watau sarki Dauda ya  dade yana bayyana mana yadda shi kansa sarki Dauda da kuma kowane dan’adama dukan an sifanta su a chikin mugunta. Sai da ya ci gaba da bayyani da cewa “Cikin zunubi kuma uwata ta dauki cikinsa”.

Anan muna tunani sarki Dauda mai zabura na nufi da cewa bayan da Adamu ya yi zunibi, to duk dan’adam da aka haifesu bayan nan, dukansu solar gaji zunubi daga Annabi Adamu. Ashe zunubi gado ne daga Adamu zuwa ga dukan Bil Adama. Kuma a rayuwan kowane dan’adama akwai cikakun shaidu ko hujjoji da suka gamsar damu cewa kowane mutum mai aikata zunubi ne ko mugunta.

Manzo Bulus ya ruwaito wa mutanen Romawa da cewa:

“Da shi ke dukan mutane solar yi zunubi solar kasa kuma ga darajar Allah” (Romawa3:23).

Amma menene dalilin da kowane  dan’adama ya yi zunubi ya kasa kuma ya darajar Allah? Mai karatu zai iya tambaya da cewa me ya yi zafi haka? To gaskiyan maganan shine, masu iya magana solar ce, tuna baya shi ne roko.” In mun tuna da baya, to zamu gane da cewa Romawa three:23 na mayar da mu baya ne, da kuma tunatar da mu da tarihin zunubi. A chikin Littafin farawa sura three, Allah Ubangiji ya bayana mana assalin zunubin dan’adama.

Daga littafin farawa sura three sai muka gan tabbacin wannan maganar a littafin farawa sura eight wanda ke cewa:

“. . . . . . Gama tunanin zuchiyar mutum mugunta ne tun daga kuruchiyassa. Ba kwa za ni sake bugun dukan mai–rai da dai, yadda na rigaya na yi” (Farawa eight:21b)

Manzo Bulus ya tabbatar mana da gaskiyar wannan maganan da marubucin littafin Farawa sura three ya ruwaito. Manzo Bulus ya nuna mana da cewa, ai tawurin zunubi na farkon da iyayenmu na farko suka aikata shine ya shafi kowane dan’adama.

Manzo Bulus ya tabbatar mana da cewa, sanadin farkon zunubi da Adamu da Hauwa’u suka aikata shine ya kai dukan Bil Adama ga faduwa daga darajar Allah (Roman three:23).

Shi kuma sarki Dauda mai zabura ya fabimci littafin Farawa three akan cewa, “Chikin mugunta aka sifanta shi, chikin zunubi kuma uwata ta dauki chikinsa.” Watau tun kafin shi sarki Dauda ya shigo duniya, ya shiga duniya cike da zunubi da ya gada daga iyayen sa. Watau duk, kowane irin Bil Adama an sifanta shi a chikin mugunta ko zunubi ne, kuma an dauki chikinsa chikun zunubi ne.

Dommin da haka baa bin mamaki ba ne, in Bil Adama solar aikata zunubi. Ina an aikata zunubi, to alama ce kowane mutum ya gaji zunubi. Duk wanda ya aikata zunubi chikon nassi ne, sai dai kawai kowa ya tuba ga Allah domin samun gafaran zunubai.

Dora da wannan, Farawa eight:21 na kara fahimtar da mu, akan gadon zunubi da ya kai dukan Bil Adama har ya baro! A littafin Farawa eight:21 an kara tabbatar mana da cewa; “tun daga kuruchiyassa, tunanin zuchiyar mutum mugunta ne” Abin tambaya anan shine, in mutum ko Bil Adama tunanin su tun daga kuruchiyarsa mugunta ne, to wanene ya koya wa mutum ko karamin yaro yin mugunta ko zunubi?.

In kwa babu wanda ya koya wa wani aikata mugunta ko zunubi tun a yarantaka, to ashe zunubi na na chikun kayan gado da ko wane Bil Adama ya gack tun daga farkonsa.

Shi kuma Annabi Irimiya, ya kawo mana wata tabbaci akan matsayin zuchiyar mutum ko Bil Adama kama yadda littafin Farawa eight:21 ya tabbatar mana recreation da yanayin zuchiyar mutum ke tattare da rikici ko zunubi ko mugunta.

Ga abinda littafin irimiya na cewa:

“Zuciyar tafi komai rikichi, ciwuta gareta kwarai irin ta fidda zuchiya: wa za ya san ta?

Ni Ubangiji mai–bimbinin zuchiya ne, ina gwada chiki, domin in saka ma kowane mutum bisa ga ayukansa, bisa ga yayan aikinsa” (Irimiya 17:9 – 10).

In wannan shine matsayin zuchiyar mutum ko dan’adama, to ashe Allah ya tabbatar mana da matsayin mu akan maganan zububi. Allah ne da kansa ya kara tabbatar mana da cewa, “Zuchiya ta fi komai rikichi”.

Domin da haka abin tambaya anan shine, Allah na karaya ko kuskure? Amsan shine Allah Ubangijinmu baya karya ko kuskure.

Wannan matsayin da Allah ya nuna mana recreation da matsayin zuchiyar mutum ya kamata ya zama mana chikakan darasi ne, domin kowa ya gyara halinsa. Wannan kiran domin gyara hali me. Wannan kira ga gyara hali shine tuban gaskiya. Kowane mutum ya yarda da matsayinsa Allah cewa mutum ne ya fada ga darajar Ubangiji Allah.

Mutum ya juyo daga mugunta zuwa neman gafaran zunubai domin samun tsiran Allah daga hallaka, amma ba kame – kame ba. Tuba daga zunubi ne kadai mafita ga dan’adama.

What's On Your Mind?