An Sauya Sunan Rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Zuwa ‘Operation Hadin Kai’

0
113

An Sauya Sunan Rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Zuwa ‘Operation Hadin Kai’

Babban hafsan sojin kasa, Janar Ibrahim Attahiru ya bayyan sauya sunan rundunar ‘Operation Lafiya Dole da ke kai tsaro a yankin arewa maso gabas zuwa rundunar Operation Hadin Kai.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce matakin yana daga sauye sauyen da babban hafsan sojin kasar ke gabatarwa da nufin kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin ya fitar Birgediya Janar Mohammed Yerima ta ce an sauya sunan ne bisa nasarorin da sojojin suka samu a tsawon shekaru da kuma bukatar sake daidaituwa ga ingantaccen aiki.

Babban hafsan sojan a cewar sanarwar ya yi imani cewa kawar da duk wani mai tawaye gaba ɗaya tsari ne da ke bukatar hadin kan kasa baki daya da kuma amfani da dukkan karfin da kasa take da shi.

What's On Your Mind?