An Samu Shuɗin Lu’u-lu’u Mafi Girma A Duniya

0
87

An Samu Shuɗin Lu’u-lu’u Mafi Girma A Duniya

Wani dunkulen shudin lu’u-lu’u mafi girma a duniya ya ja hankalin jama’a da dama, amma abin tambaya shi ne ya aka yi har wannan dutse ya yi wannan girma?

Ga Nazarin Melissa Hogenboom

An bayyana dunkulen shudin dutsen mafi girma a duniya, wanda aka gano a yankin hakar ma’adanai na Ratnapura da ke Sri Lanka.

Masana ilimin kimiyyar duwatsu masu daraja na kasar solar ce ba su taba ganin dunkulen shudin daimon da ya kai kusan giram 280 ba.

Ana kiran wannan dutse da suna ”Star Sapphire” wato shudin lu’u-lu’u mai tauraro, saboda tauraro mai kusurwa shida da ake gani a cikin dutsen.

Mai dutsen wanda ba a bayyana sunansa ba ya ce za a iya sayar da shi a kan Dalar Amurka miliyan 175.

BBC ta tuntubi masanin kimiyyar albarkatun kasa Simon Redfern na jami’ar Cambridge a Burtaniya domin sanin girman da irin wannan dutsen zai iya yi.

“Samuwar wannan dutse abu ne da ke daukar dogon lokaci. Kuma ana ganin wannan dunkulen mafi girma ya samu ne a duwatsun tsaunukan Sri Lanka.

Duwatsun tsaunukan yawanci suna samuwa ne daga talgen dutse a lokacin da ya yi san yi ya daskare. Wadannan duwatsu ana ganin solar kai shekara miliyan dubu biyu da suka wuce, sannan kuma daga baya sai suka samu wani sauyi na yanayin inda suke sama da shekaru miliyan 500 da suka wuce,” in ji Redfern.

Akwai tsananin zafi da ya kai lamba 900 a ma’aunin digirin selshiyas (900C) da kuma nauyin iska da ya kai lamba 9000 a gindin wadannan tsaunuka.

Redfern ya ce wannan tsananin zafi da iska da ke wurin su za su iya sa dutsen mai daraja ya yi girma sosai kamar yadda aka gan shi.

Bayan dutsen mai daraja ya samu, sai ya zauna a cikin manya-manyan duwatsun tsaunin, har zuwa lokacin da za su taso zuwa tsaunukan, inda daga nan kuma sai ruwa ya wanko su zuwa kasa, har su kai zuwa yashin kogunan yankin na Ratnapura, kamar yadda Redfern ya ce.

Ya ci gaba da cewa “Duwatsu masu daraja irin wadannan suna jure wa irin wannan tafiya ne mai wuya saboda suna da karfi sosai, amma duwatsun da ba su kai su karfi ba ruwa ya kan tafi da su ne su bata a cikin tabo da yashi, inda a kan similar su a gabar kogin Sri Lankan.”

 

What's On Your Mind?