Cikar Nijeriya 60: An Sami Nasarar Dorewar Dimakwaradiyya Da Cigaba -Hon. Garba Bullet

0
46

Cikar Nijeriya shekaru 60 da samun mulkin kai abune daya kamata duk dan kasa yayi  farin ciki musamman masu yawan shekaru daya wuce 60 a Duniya zai tabbatarda cewa an sami dorewar mulkin Damakwaradiyya a wannan lokaci da ake ciki. Dan majalisar jaha mai wakiltar Garki.Bulaliyar mmajalisar Dokokin Jihar  Jigawa.Hon. Lawan Garba  Bullet ya bayyana haka a lokacinda ya halarci bukin samun yancin kai a Kano.

Ya ce wadannan shekaru photo voltaic  tabbatarda cikar kasarnan na kaiwa gaya na girma,domin ta haura shekaru da tasowa, kuma a cikin walwala da zaman lafiya bisa kokarinda shugabanni da suka mulki kasarnan sukayi a lokuta daban-daban na mulkinsu.

An Sami Nasarar Dorewar Dimakwaradiyya Da Cigaba -Hon. Garba Bullet

Sai  dai Hon.Lawan Garba Bullet yayi kira ga shugabanni akan suyi kokarin  daukar matakin na kawo sassauci a irin halin kuncin rayuwa da ake ciki a wannan lokaci  duk da cewa wani tsarine na Ubangiji daya kawo amma da dagewa wajen yin  addu’oi daga  jama’a  da Malamai da shugabanni za’a samu a wuce wannan matsalar da ake ciki.

Su kuma mabiya shugabanni su cigaba da addu’a domin ganin an sami nasara kawo karshen matsaloli da ake fuskanta a kasarnan a halin yanzu.

Wajibine ayi farin ciki a wannan kasa da samun yanci in aka duba  yanda aka taho kai a  hade babu wani kace nace.Saboda ko wani abu ya taso inya  yunkuro ana kace nace akai  saboda karfi na addu’a da ake sai abin  ya kwaranye a sami mafita da maslaha akai.

Jarumi Lawal Ahmad – Shirin ‘Izzar So’ Ya Zama Garkuwa Ga Mutuncin Masana’antar Kannywood

Bulaliyar na majalisar dokokin jihar Jigawa Hon. Muhammad Lawan Garba Bullet ya ce an sami cigaba sosai a kasarnan domin ko ‘yan sanda da suke fareti ai da sunayi ne da gajeren wando  amma saboda sauyawa daga wannan yanayi zuwa wani sabo yanzu  gashi da dogon wando suke a wannan fili da ake bukin,ga NYSC masu yiwa kasa hidima da suka fito daga lunguna daban-daban na kasarnan wannan kuma  tsarine na hadin kan kasa da cigabanta da aka bijiro dashi dan hadin kai.

Hon.Bullet yayi nuni da cewa  al’ummar Nijeriya nada dinbin yawa.Duk kasarda take da irin wannan al’umma cigabanta sai a hankali yake zuwa saboda za’a sami yawan matsaloli da kuma kokarin magancesu, amma duk da haka ana yin abinda yakamata dan cigaban kasa.Duk  kukan ana wani hali na kuncin rayuwa da ake  in akayi la’akari da yanda aka sami  dorewar Damakwaradiyya a Nijeriya za’a ga lallai ta sami cigaba babba.

Hon.Muhammad Lawan Garba Bullet wanda tsohon shugaban  karamar hukumar Garki a Jihar Jigawa kafin zamansa dan majalisar jaha yayi rokon Allah ya cigaba da wanzarda kasarnan ta sami cigaban hadin-kai da zaman lafiya da yalwatar tattalin arzikinta da kowa zai amfana dukkan matsaloli su kau.

Bulaliyar majalisar Dokokin a majalisar jihar Jigawa.Hon.Bullet ya ce Jihar Jigawa tunda aka kirkiro jihar Jigawa ba’a taba samun majalisarda take cin gashin kanta ba sai a karkashin Gwamna Badaru Abubakar.

Ya ce yana alfahari duk a jahohin Arewa maso yamma ba wata jaha da dan majalisa yake samun dama yayi aiki a mazabarsa irin a jihar Jigawa. Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar adaline da ilimi mai hangen nesa shi yasa ma a zabensa karo na Biyu ba’asha wahala a tallata manufofinsa ba sabosa mutane photo voltaic gani a kasa.

Hon.Bullet yayi nuni da lokacinda aka kirkiri Jihar Jigawa wasu ma basa so kai ya rabu,amma da tafiya tafiya tayi nisa kai ya hadu.

Yanzu kowa a kasarnan yanda suke da sanatoci uku haka Jigawa take dasu haka ma yan majalisar jaha dana tarayya.

Hon.Lawan Garba ya ce yanzu a Jihar Jigawa zancen cigaba a matakin kananan hukumomi ya wuce a matakin cigaban mazabu ake ba inda zakaje a jihar kaga ba ruwa ba kwalta ba wutar lantarku kuma ba Asibiti wannan shi ne babban cigabanda aka  samu daga nan zuwa karshen shekara Uku za’a sami cigaba daya nunka wanda ake samu a yanzu

What's On Your Mind?