An Sada Layukan Waya Miliyan 190 Da Katin Dan Kasa Zuwa Yanzu – NCC

- Advertisement -

An Sada Layukan Waya Miliyan 190 Da Katin Dan Kasa Zuwa Yanzu – NCC

Hukumar Kula da Sadarwa ta kasa ta bayyana cewa akalla layukan waya 190 ne ake da yakinin an sada su da katin shaidar zama dan kasa a yayin da kusan mutum sama da miliyan 50 suka mallaki katin dan kasan.

Har ila yau, hukumar ta ce Gwamnatin Tarayya ta amince da karin wa’adin hada lambar waya da katin shaidar zama dan kasa har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2021.

kara wa’adin ya zo bayan kammala wani taro ta hoton bidiyo da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Fasahar Zamani, Dafta Isah Ali Ibrahim Pantami ya shugabanta tare da Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Adeolu Akande, da Babban Shugaban Gudanarwar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta da sauran mahukuntan sashen aikin katin shaidar zama dan kasa.

karin wanda mai magana da yawun NCC, Ikechukwu Adinde and Kayode Adegoke, ya tabbatar a wata sanarwa, an yi ne a cewar hukumar bisa rokon da masu ruwa da tsaki suka yi wadanda suka kafa hujjar cewa idan aka mayar da karshen wa’adin zuwa 30 ga Yuni ‘yan kasa nagari da sauran mazauna kasa za su samu damar yin rajista cikin sauki.

“An samu ci gaba a aikin sada lambar waya da katin shaidar zama dan kasa. Misali, a yanzu mutum kusan miliyan 54 ne suka yi rajistar katin dan kasa kuma wannan za a iya cewa solar sanya an samu katin lambar waya da aka yi rajista da katin kusan miliyan 190, saboda shaidu solar tabbatar da cewa a kowane katin shaida ana iya samun layukan waya akalla uku da aka sada su da shi.

Sanarwar ta kara da cewa masu kamfanonin waya da sauran wakilan gudanar da rajistar katin dan kasa a sassan kasar nan solar kara bude cibiyoyin rajista domin ‘yan kasa su samu su yi cikin sauki.

- Advertisement -