An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

0
148
  • Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano tayi nasarar ceto rayuwar mata 3, sai dai kash, mata daya ta rasa ranta

  • Sabon ginin shagon bene da aka yi a kasuwar Kurmi, ya ruguzo wa mata 4 da suka je siye da siyarwa

  • Al’amarin ya faru a ranar Asabar din da ta gabata, ya kai ga raunata mata 3 da kashe mace

Hukumar kashe gobarar jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata sakamakon rushewar da wani sabon shago da ake ginawa a kasuwar Kurmi yayi.

Shagon ya fado wa mata 4 dake wucewa ta wurin ginin a ranar Asabar da ta gabata.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sa’idu Haruna, ya ce an kira su ta waya, inda aka sanar da su rushewar shagon.

Wani mai gani da ido, Malam Jadda Bashir, ya sanar wa manema labarai cewa, duk wadanda ginin ya fada wa mata ne, sunzo siye da siyarwa.

Kamar yadda ya ce, sabon ginin bene ne aka yi, sai dai anyi rashin sa’a ya ruguzo.

An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

Ya ce inda Allah yayi taimako ba a ranakun mako bane al’amarin ya faru ba, da wadanda zai shafa sai solar fi haka

A wani labari na daban, ‘yan sandan jihar Adamawa solar damke wata matar aure da ake zargi da yi wa diyar mijinta dukan da yayi ajalinta.

Hatsarin mota ya halaka rayuka 9 a Kano

Aishatu Umaru ta shiga hannun hukuma a ranar Alhamis bayan makwabta solar kai wa ‘yan sanda koken zarginta da suke da

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje wanda ya zanta da manema labarai a Yola, ya tabbatar da kamen Aisha Umaru daga kauyen Kugama da ke karamar hukumar Mayobelwa ta jihar a kan laifin horo da yunwa da kuma kashe yarinyar.

What's On Your Mind?