An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Alumni Na Isa Mustapha Agwai A Nasarawa

0
51

An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Alumni Na Isa Mustapha Agwai A Nasarawa

Kungiyar Alumni dake makarantar kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai dake Lafia jihar Nasarawa ta ranatsar da sabbin Shugabannin a ranar Litinin 11 ga Janairu, 2021.

Bayan zaben sabbin Shugabannin da aka gudanar a ranar 12 ga watan Dusambar shekarar 2020.

Kungiyar ta zabe sabbin Shugabannin su takwas bisa yadda tsarin mulkin kungiyar ya tabbatar da mukaman Shugabannin kungiyar.

Kalli Zafaffan Hotunan Maryam Yahya Yar kwalisa

Bayan rantsar da sabbin Shugabannin, tsohon Shugaban kungiyar Jamilu Abubakar ya nuna godiya da yadda ya’yan kungiyar suka gudanar da zaben sabbin Shugabannin bisa tsari da inganci.

Ya kuma yi fatan sabbin Shugabannin zasu cigaba da jan ragamar kungiyar bisa tafarkin gaskiya da rikon amana.

Ya kuma yi godiya ga membobin kungiyar saboda goyon bayan da suka basu na gudanar da nasu mulkin zuwa adadin karewar su ga jagoranci. Daga bisani ya mika ragamar kundin tsarin mulki ga sabon shugaba.

Shi ma sabon shugaban kungiyar Mista Ogbole Arenya ya yi godiya ga Membobin kungiyar da suka bashi dama domin jagorantar su.

Ya kuma yabawa tsofin Shugabannin kungiyar saboda yadda suka jajirce har kungiyar ta kafu da kafarta.

Ya kuma godewa Hukumar zaben da ta gudanar da zaben bisa inganci.

Yayi kira ga sauran membobin kungiyar dasu zo a hada kai a tafi tare domin cigaban wannan kungiyar da Makarantar kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai.

Ya ce za su kawo sauyi mai mahimmanci ga wannan makarantar da hadin kai domin gudanar da ayyuka tare da Shugabannin makaranta da duk wani fanni na jagororin dake makarantar harma da bangaren dalubai.

Ya kara da cewa burinsu tabbatar da adalcine ga kowa da kowa dake kungiyar dama wannan makaranta

What's On Your Mind?