Ruga-kafin Korona: An Nemi ‘Yan Nijeriya Su Kara Bayar Da Hadin Kai

0
154

An Nemi ‘Yan Nijeriya Su Kara Bayar Da Hadin Kai

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin kasashen waje, Mr Yusuf Buba (APC-Adamawa), ya bukaci ‘yan Nijeriya su bayar da hadin kai ga harkar rigakafin cutar korona da ake yi a halin yanzu don dakile barazanar yaduwar cutar a fadin kasar nan, ya bayyana haka ne bayan da aka yi masa allurar rigakafin samfurin ‘Oxford Astrazeneca’ a asibitin fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a.

Dan majalisar wanda yake wakiltar mazabar Gombi/Hong ya ce, dole a hada hannun don kawo karshen yadda cutar ke yaduwa a faxin kasar nan musamman a cikin shekarar da ta wuce.

Gaskiya Gwamnatin Jihar Kano Bata Kyautawa Khalifa Sheikh Mahi Inyass Da Sauran Shehunnan Tijjaniyya Ba

“Ina amfani da wannan damar na kira ga ‘yan Nijeriya su bayar da hadin kai ga shirin allurar rigakafin cutar korona musammna ganin yadda ta addabi duniya gaba xaya a shekarar da ta gabata.

“Wannan kiran ya sama dole musamman ganin jita jitar da ake yaxawa na cewa, allurar nada illa ga rayuwar al’umma.

“Kafin a fara amfani da allurar sai da NAFDAC ta tabbatar da ingancin allurar saboda haka babu wani matsala a yin allurar,” inji shi.

Daga nan ya kuma yaba wa waxanda suka kirkiro allurar (COVAX) da kuma hukumar lafiya ta duniya (WHO) akan matakin da suka dauka na dakile cutar a faxin duniya gaba xaya..

What's On Your Mind?