An Nada Mukaddashin Kwamandan Hisba A Karamar Hukumar Kumbotso

0
69

An Nada Mukaddashin Kwamandan Hisba A Karamar Hukumar Kumbotso

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

 

Sakamakon dakatar da tsohon kwamandan Hukumar Hisba na karamar Hukumar kumbotso kwanakin da suka gabata bisa wasu korafe korafe da suka yawaita akansa, a ranar litinin information gabata shugaban karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban kauye Farawa ya amince tare da nada sabon Mukaddashin kwamanda Gwani M. Ahmed Jarumi wanda zai ci gaba da jigorantar ayyukan Hukumar a karamar Hukumar Kumbotso.

Alhaji Hassan Garban kauye Farawa ya ja  hankalin sabon kwamandan kan  ya tsaya  ya yi  aiki  bisa  gaskiya  da rikon  amana. Kasancewar  aikin  Hisbah  aiki ne  na  Allah, saboda haka Shugaban ya jaddada aniyar Gwamnatinsa na yin Aiki ka’in da na’in da bangaren Hukumar ta Hisba domin inganta rayuwar al’umma.

Shima sabon Mukaddashin kwamandan ya yi alkawarin yin aiki kamar yadda doka ta tanada, sannan ya godewa Shugaban karamar Hukumar ta Kumbotso bisa bashi wannan dama domin bayar da tasa gudunmawar. A karshe ya bukaci hadin kan abokan aikinsa domin samun nasarar aikin. Nadin nasa ya fara aiki nan ta ke. Kamar yadda jami’in yada labaran karamar Hukumar Kumbotso Nasiru Wada Agasawa ya Shaidawa MOBILIZED9JA A Yau.

What's On Your Mind?