An Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iayayensu

- Advertisement -

An Mika Daliban Makarantar Afaka 27 Ga Iayayensu

Daga Mustapha Abdullahi,

Kamar yadda bayani ya gabata a tun shekaran jiya cewa cikin hukuncin Allah daliban makarantar Koyar da aikin Gona da al’amuran Gandun daji solar samu kubuta daga hannun yan bindigar da suka sace su a wani Dare cikin harabar makarantar da ke Unguwar Afaka karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Yau ne dai aka mika su ga iyayensu, inda wurinbya impolite da koke-koken murna da farin ciki.

Kamar yadda zaku iya gani a cikin hoton nan daliban ne a cikin ingantattun kaya masu kyau da tsada wasu na ta kuka domin murnar sake haduwa da iyaye da yan uwa tun bayan da aka sace su a cikin makarantar inda suka kwashe tsawon kusan watanni biyu a hannun yan bindiga a cikin daji.

Daliban dai solar yi bayanin cewa tsawon zamansu a wurin yan bindigar ana ba su Tuwo miyar kuka sau daya a rana inda suka tabbatarwa manema labarai cewa babu dai maganar ingantaccen abinci ko kadan.

- Advertisement -