An Maka Sheikh Daurawa Kotu


Wani mutum mai suna Malam Dauda Muhd Lokon Maƙera ya maka fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a Babbar Kotun Shari’ar Muslunci mai zama a Shahuci bisa zargin cin amana.

Malam Lokon Maƙera ya yi iƙirarin cewa shi ne mamallakin shahararren shirin nan na Musulunci da ake gabatarwa a gidajen rediyo mai suna Tambaya Mabuɗin Ilimi, kuma shi ne tsani tsakanin mai ɗaukar nauyin shirin, Sani Kwangila Yakasai.

Mai ƙarar ya yi zargin cewa Sheikh Daurawa ya wallafa wannan shiri zuwa littafi da faifan CD, ya kuma siyar da su a kasuwa ba tare da izininsa ba.

Ya ƙara da cewa wannan abu da wanda ake ƙara ya yi ya shafi ikonsa na mallakar shirin.

Ya yi kira ga kotun da ta yi amfani da ikonta wajen tabbatar da cewa an yi adalci.

A lokacin da aka zo don fara sauraron ƙarar a jiya Talata, mai ƙara ya shaida wa wa kotu cewa har yanzu sanarwa ba ta samu Sheikh Daurawa ba, yana mai bayyana cewa fiye da wata ɗaya kenan yana neman wanda ake ƙara amma har yanzu yanzu bai similar shi ba.

Lauyan mai ƙara, Barista Jafar Nuhu ya roƙi kotun da ta gabatar da sanarwa ga wanda ake ƙara ta hanyar kafe sanarwar a ƙofar gidan Sheikh Daurawa.

Kotun ta amsa wannan buƙata, ta kuma ɗage ƙarar zuwa 20 ga Oktoba, 2020 don ci gaba da sauraro.

 759 total views,  3 views today

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*