An Kashe Maciji Ba A Sare Kansa Ba: Fargabar Boko Haram Karo Na Biyu?

0
142

An Kashe Maciji Ba A Sare Kansa Ba: Fargabar Boko Haram Karo Na Biyu?

A baya gwamnatin Nijeriya ta sha yin ikirarin murkushe kungiyar Boko Haram, hana kungiyar rawar gaban hantsi tare da dakile yunkurin sake mamaye wasu yankuna a baya. Wannan ya na zuwa ne baya ga yadda mayakan suka karbe iko da wasu kananan hukumomi da daman gaske a wasu jihohin arewa maso gabas- Borno, Adamawa da Yobe, wanda sai da jibin goshi sojojin Nijeriya suka sake yanto yankunan.

A halin da ake ciki yanzu, ana murnar an raka bako bayan gari, ashe bai je ko’ina ba, sai gashi yana neman ya dawo sabo fil, saboda yadda mayakan ke ci gaba da kai sabbin hare-hare a sassan kasar nan daban-daban, wanda ko shakka babu akwai kalubale da babbar barazanar rikicin Boko Haram karo na biyu, wanda munin shi zai zarta na farko ta la’akari da mawuyacin halin da rikin ya jefa yan Nijeriya a farkon barkewar shi. Wanda wannan ya faru ne biyo bayan yadda yan ta’adsan ke ci gaba da aiwatar da kai hare-hare a bangarorin kasar nan, sabanin a shekarun baya wanda suka takaita da arewa maso gabas.

A tsakanin shekarar 2014 da 2015, daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankula da cin kasuwa a fagen siyasar Nijeriya- musamman a lokacin yakin neman zaben 2015, shi ne tabarbarewar tsaron da ya tagayyara al’amurran yankin tare da fargabar bazuwar matsalar tsaron a hannun tsohuwar gwamnatin. Hakan ya jawo wa jam’iyyar PDP mai mulki a karkashin Dr. Jonathan, hadi da zarge-zarge kala-kala.

A karon farkon matsalar, Boko Haram ta fara da kai wa ofisoshin yan-sanda da na sauran jami’an tsaro farmaki, wanda ya jawo asarar dubban rayuka, asarar dimbin dukiya ta dubban biliyoyin naira, tilasta wa miliyoyin jama’ar yankin kauracewa garuruwan su da rayuwa a matsugunan yan gudun hijira. Haka kuma, matsala ce wadda ta tagayyara yankin da jawo hannun agogo baya a yanayin rayuwar jama’a.

A baya, yan Nijeriya solar shaidi yadda aka samu ci gaba a yaki da rikicin Boko Haram tare da samun dimbin nasarori a bangarori daban-daban a yankin, ciki har da nasarorin da sojojin Nijeriya suka samu na sake kwato kusan dukan yankunan da suke a hannun mayakan, tare da aikin sake mayar da wasu dubban yan gudun hijira zuwa garuruwan su da daukar ingantattun matakan tsaro. Kana da yadda hakan ya dawo da hankalin yan kasa hayyacinsu ta hanyar kwanciya da ido daya.

Tun a wancan lokacin, an sha jin korafe- korafen ci gaba da dorewar nasarar da aka samu na fattatakar mayakan, wanda ya hada da rashin nagartattun makaman yaki, rashin samun cikakken kula da hakkokin jami’an tsaron da ke bakin fama suna yaki da yan ta’adda kana uwa uba da rashin cikakken hadin kai tsakanin jami’an tsaro a kansu, tare da yadda ake samun kusakurai tsakanin sojojin sama da na kasa, wanda hakan ya jawo gagarumar koma baya kuma babban cikas a yaki da matsalar tsaron, baya ga rashin aminci tsakanin jami’an tsaro da talakawa, matsala mafi muni da barazana a sha’anin yaki da matsalar tsaron.

An sha samun takon saka tsakanin bangarorin jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro al’amarin da ya jawo tafiyar hawainiya a yakin, ta hanyar zargin juna tsakanin sojoji da kansu kana da tsakanin sauran jami’an tsaro cike da zargin juna wajen kawo tarnaki a tsaron. Sannan da rashin hadin kai tsakanin jami’an tsaro da jama’ar wanda hakan ya jawo rashin samun ingantattun bayanan da zasu taimaka wa jami’an tsaro a aikin da suke na samar da dawamamen tsaro a garuruwan da ke fuskantar barazanar tsaro. Dangane da wannan, an sha samun korafe-korafen yadda wasu daga cikin jami’an tsaro ke cin zarafinsu, wanda hakan ya kasance babban cikas.

Bugu da kari kuma, an sha bayyana zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa wanda ya kanannade rundunonin tsaro, a matsayin tarnaki ga yaki da Boko Haram. Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sha zargin cewa akwai wasu a cikin gwamnati da jami’an tsaro wadanda ke yi wa yakin da ake yi da Boko Haram zagon kasa a arewa maso gabas da sassan kasar nan daban-daban. Wanda a yan kwanakin nan, babban mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaro (NSA), Janar Babagana Monguno ya yi zargin wasu solar handame biliyoyin naira da gwamnatin Buhari ta have been domin sayo makaman da za a yaki Boko Haram da su.

A hannu guda kuma, tabarbarewar tsaro ta fara da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Nijeriya wanda daga bisani ya rikide zuwa karin wasu sabbin matsalolin tsaro wadanda suka fara da rikicin makiyaya da manoma, yan bindiga dadi, barayin shanu, masu garkuwa da jama’a wanda ya shafi kowane lungu da sakon kasar nan, al’amarin da ya kara zurfin matsalar da addabar kowa a kasar nan.

Wadannan da makamantan su, su ne kashin baya da mayar da hannun agogo baya a yakin da ake yi da rikicin Boko Haram wanda yana bukatar sake bin bahasi da samun sauyi a halin da ake ciki. Saboda a watanni biyu da suka gabata zuwa yau, hare-haren Boko Haram solar tsananta a jihohin Borno da Yobe kana da wasu yankuna a arewa maso yamma da sauran su, wanda hakan tamkar kashe maciji ne ba a katse kansa ba.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ja hankalin gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye haikan wajen daukar sabbin ingantattun matakai a yaki da matsalar tsaron yan ta’adda wadanda suka addabi kasar tare da bukatar cewa bayan amfani da sojoji a hada da sabbin matakai da salon yaki don maganceta baki daya a kasar.

Da yake yi wa manema labarai bayani, shugaban tawagar kungiyar a Nijeriya tare da sauran kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), Amb. Ketil Karlsen, ya kara da cewa ci gaban kalubalen tsaro a Nijeriya ya tabbatar da cewa karfin bindiga kadai ba zai kasance mafita ta karshe wajen shawo kan matsalar ba, baya ga ita akwai hawa teburin sulhu da sauran matakan da shari ‘a ta lamunta dasu a kokarin magance matsalolin tsaro a duniya.

Ya ce bayar da shawarar amfani da zaman sulhu da kungiyar Tarayyar Turai keyi ba yana nufin kokari wajen karfafa gwiwar yan ta’adda bane face kawai domin nemo wasu hanyoyin shawo kan matsalar a kasar. Tare da karin haske kan cewa kungiyar ta zaku matuka wajen lalabo mafita dangane da kalubalen tabarbarewar tsaro a Nijeriya.

What's On Your Mind?