An Kashe Jami’an ‘Yan Sanda Tara A Jihar Kebbi

0
127

An Kashe Jami’an ‘Yan Sanda Tara A Jihar Kebbi

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da mutuwar wani jami’inta mai matsayin DPO da jami’ansa takwas a Jihar Kebbi. Kakakin ‘yan sanda na Jihar Kebbi ASP Nafi’u Abubakar ne ya tabbatarwa manema labarai da faruwar lamarin, wanda ya faru a jiya Lahadi.

“Da misalin karfe 2:30 na rana ne DPO na Kasaba ya samu labarin an kai hari wani kauye da ake kira Makuku da wasu kauyuka da ke kewaye da shi, nan da nan ya debi jami’ansa su takwas da nufin kai dauki bayan fafatawa kuma anan suka gamu da ajalinsu,” in ji ASP Nafi’u.

What's On Your Mind?