An kashe dan sanda daya a yayin da zanga-zangar neman rushe SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi 3

0
61
  • Yan Najeriya na cigaba da nuna fushinsu tare da neman gwamnati ta soke rundunar ‘yan sandan SARS da aka kafa domin yaki da fashi da makami

  • Ma su neman a soke SARS su na zargin jami’an rundunar da aikata laifukan da aka kafasu domin su yaka

  • A yayin da aka shiga rana ta biyu da fara gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, an samu barkewar rikici tsakanin jami’an tsaro da fararen hula

An samu barkewar rikici a Abuja, Delta, da Osun yayin zanga-zangar neman a kawo karshen ‘yan sandan SARS da kuma nuna kyamar zaluncin jami’an ‘yan sanda.

Jaridar Punch ta rawaito cewa ‘yan sanda solar yi harbe-harbe domin tarwatsa ma su zanga-zangar.

A Osogbo, babban birnin jihar Osun, zanga-zangar ta haddasa cunkuso a babbar kwanar Ola-Iya.

Rahotanni solar bayyana cewa ma su zanga-zanga solar yi ruwan duwatsu a kan jami’an ‘yan sandan da ke kokarin hanasu cigaba da gudanar da tattakin da suka fara.

An kashe dan sanda daya a yayin da zanga-zangar neman rushe SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi 3

Jaridar TheCable ta rawaito cewa an kashe wani dan sanda, Etaga Stanley, mai mukamin kofur, yayin zanga-zanga a jihar Delta ranar Alhamis.

Mutane da dama da suka hada da jami’an ‘yan sanda solar samu raunuka yayin zanga-zangar.

Yadda na rusa kuka saboda irin abin da aka rika yi mani a Barcelona – Luis Suarez

TheCable ta ce babu wani bayani sahihi dangane da dalilin kisan dan sandan, wanda aka samu gawarsa a yashe cikin kaskanci a kan wani titi da ke Delta.

Sai dai, babban sifeton rundunar ‘yan sanda (IGP), Muhammed Adamu, ya ce ba za su yarda da cin zarafin jami’an ‘yan sanda da sunan zanga-zanga ba.

What's On Your Mind?