An Karyata Rahoton Dake Ikirarin Ana Kokarin Maye Gurbin Alummar Jihar Xinjiang Da Kabilar Han

0
59

An Karyata Rahoton Dake Ikirarin Ana Kokarin Maye Gurbin Alummar Jihar Xinjiang Da Kabilar Han

Daga  CRI Hausa

Cibiyar bincike da raya jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta arewa maso yammacin kasar Sin, ta fitar da wani rahoto da ya karyata ikirarin Adrian Zenz, dan kasar Jamus dake cewa, ana wani nauin mulkin mallaka na maye gurbin mutanen Xinjinag da yan kabilar Han a jihar.

Adrian Zenz ya yi ikirarin cewa, karuwar yawan alummar kabilar Han a yankin Gulban na birnin Hotan ya kai 151.7 cikin 1,000 a shekarar 2018, yayin da na yawan karuwar mutane a gundumar Hotan ya ke matsayin 2.22 cikin 1,000.

Sai dai kididdiga daga yankin Hotan ta nuna cewa, yawan karuwar alummar kabilar Han a Hotan ya tsaya ne kan 1.2 cikin 1,000 a 2018 yayin da karuwar yawan alumma a gundumar Hotan yake matsayin 5.29 cikin 1000. (Mai Fassara: Faiza Mustapha)

What's On Your Mind?