An Kama Barayin Motar Jarumi Nasiru Naba, Har Da Maƙwabcin Sa Cikin Barayin

0
157

An Kama Barayin Motar Jarumi Nasiru Naba, Har Da Maƙwabcin Sa Cikin Barayin

KWANA 12 da sace motar jarumin Kannywood Nasiru Bello Sani (Nasiru Nava), ‘yan sanda sun samu nasarar kama ɓarayin motar su bakwai.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a ranar 31 ga Maris, 2021 na yadda wasu waɗanda ba a san ko su waye ba su ka haura zuwa gidan jarumin a unguwar Maidile a Kano su ka ƙwace masa kayayyaki, ciki har da motar da ya saya da kwana ɗaya.

A jiya Asabar, ‘yan sandan a Kano sun yi holar ‘yan fashin da su ka haura gidan matashin jarumin na cikin shirin fim nan mai dogon zango na ‘Labari Na’ wanda ake nunawa a tashar talbijin ta Arewa24.

‘Yan sandan sun nuna ‘yan fashin a wani bidiyo da su ka ɗauka a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano da ke unguwar Bompai, wato su huɗu tare da masu taimaka masu wajen sayen kayan sata mutum biyu, sai kuma matar ɗaya daga cikin ɓarayin wadda ke adana masa bindiga a tsawon shekaru.

Jarumar yarinya tana fatattakar kattin ‘yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda

Waɗanda aka kama ɗin da shekarun su na haihuwa su ne: Sa’idu Abubakar (32) da matar sa Zainab Abubakar (20); Isyaku Maude (28), Adamu Ya’u (32), Sulaiman Jaafar (24), da masu sayen kayan sata, wato Kabiru Abubakar da Ibrahim Hassan (27).

Da ya ke ƙarin haske kan lamarin a faifan bidiyon da ya ɗauka, wanda mujallar Fim ta samu kwafe, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi bayani kamar haka: ”Biyo bayan umarnin da kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, na faɗaɗa sintiri da kuma aiki kafaɗa da kafaɗa tare da al’umma, Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki ya ba mu nasara.

“A ranar 29 ga Maris, 2021, da misalin ƙarfe 2:30 na dare, mun samu rahoto daga wani bawan Allah da ke zaune a unguwar Maidile a nan Kano kan cewa ‘yan fashi da makami sun shiga gidan sa da bindigogi da sauran makamai, su ka ƙwaci kayayyakin sa da kuma yi masa fashin motar sa mai suna Ford, ja.

”Bayan samun ƙorafin ne kuma kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya tada rundunar ‘Operation Puff Adder’, wanda kuma Allah Ya ba mu nasara mu ka fara kama waɗannan mutane guda huɗu.

“Lokacin da mu ka kama su, mun kama su da makamai kamar bindigogi biyu, harsasai guda 38, da wuƙaƙe da kuma wasu daga cikin kayayyakin da mu ka kama su da su, tare kuma da mutanen da su ke sayen kayan da ‘yan fashin su ka sato.”

Kiyawa ya ƙara da cewa, “Tuni kwamishinan ‘yan sandan Kano ya bada umarni a kai su sashen aikata manyan laifuffuka domin a faɗaɗa bincike.”

An ba ‘yan fashin dama su maida jawabi ɗaya bayan ɗaya a lokacin da Kiyawa ke masu tambayoyi a gaban motar da su ka sata.

Daga bayanan su, an fahimci cewa aun daɗe su na aikata muggan laifuffuka a Jihar Kano da wasu jihohin.

Haka kuma an fahimci cewa tare da wani maƙwabcin jarumi Nasiru Naba, wani mai suna Sulaiman Jaafar, ɓarayin su ka haɗa baki wajen aikata ta’asar, inda ya sanar da su gidan jarumin domin su je su yi masa fashi.

An Kama Barayin Motar Jarumi Nasiru Naba, Har Da Maƙwabcin Sa Cikin Barayin

A cewar su, bayan sun yi satar motar da wayoyin jarumin da kwamfutar sa, sun garzaya zuwa Jihar Sakkwato domin su sayar da motar, to amma haƙar su ba ta cimma ruwa ba, ‘yan sanda su ka cafke su.

A jawabin sa, jagoran ‘yan fashin, Sulaiman Jaafar, ya faɗi yadda ya gayyato ‘yan fashin, ya ce: ”Abokai na ne, su ka kira ni su ka ce na zo mu je na nuna musu inda za mu je a yi fashi mu samu kuɗi, inda kuma na nuna musu gidan maƙwabcin nawa, su ka kuma shiga da daddare su ka ɗauki kwamfuta da wayoyin sa da kuma motar sa. Kuma layin mu ɗaya da shi.”

A nasa ɓangaren, Nasiru Nava ya bayyana farin ciki bisa wannan nasara da ‘yan sandan su ka samu.

Ya faɗa wa ‘yan sanda a bidiyon cewa: ”Ina jin farin ciki bisa wannan nasara da aka samu. Kuma ina ba wa mutane shawara daga zarar wani abu ya faru, su yi ƙoƙarin sanar da hukuma, su yi addu’a Allah Ya bayyanar da gaskiya.

”Sannan ina roƙon gwamnati da ta yi musu duk abin da ya dace. Ta ɗauki mataki mai tsauri ta yadda wasu ba za su yi sha’awar shiga irin wannan aikin ba.”

What's On Your Mind?